Legas za ta karbi wasan Super Eagles a karon farko bayan shekara 20

Super Eagles

Asalin hoton, Pooza Media

An wallafa

Jihar Legas za ta karbi bakuncin wasan tawagar kwallon kafa ta Najeriya a karon farko tun bayan shekara 20.

Super Eagles za ta kara da Lesotho ranar 30 ga watan Maris a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za su yi a Teslim Balogun.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta ce yawan mutanen da za su kalli karawar ya ta'allaka kan matakan hana yada cutar korona da hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF da za fitar kan lokacin wasan.

Wasa na karshe da Super Eagles ta buga a Legas shi ne a Janairun 2001 wanda ta doke Zambia a fafatawar shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Sai dai a shekarar 2011, Najeriya ta buga wasan sada zumunta da Saliyo, inda ta yi nasara a filin Teslim Balogun a jihar ta Legas da ci 1-0.

Ministan wasanni na Najeriya, Sunday Dare ya ce filin wasa na Legas zai ci gaba da karbar bakuncin wasannin kasar da zarar an kammala gyaran katafaren filin.

Super Eagles ta ci gaba da yin wasanninta a wasu jihhohin fadin kasar, bayan da hukumar kwallon Najeriya, Nff kan tuntubi wadda keda sha'awar karbar bakuncin wasannin.

Duk jihar da ta karbi bakuncin Super Eagles kan taimaka da kudi wajen gudanar da wasannin kamar yadda ta buga a Port Harcourt da Kano da Cross River da Akwa Ibom da Delta da kuma babban birnin tarayya Abuja.