Barca za ta kara da PSG a wasan zagayen farko a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Za a ci gaba da wasannin zagaye na biyu a Champions League wasan farko, inda Barcelona za ta karbi bakuncin Paris St Germain a Nou Camp ranar Talata.
Barcelona ta kawo wannan matakin ne, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na bakwai, ita kuwa PSG ita ce ta ja ragamar rukuni na takwas a wasannin bana.
Barcelona wadda ta yi wasa 22 a gasar La Liga mai maki 46, tana ta uku a kan teburi, PSG kuwa wadda ta buga karawa 25 a Ligue 1 tana ta biyu da makinta 54.
Kungiyar ta Nou Camp ta lashe Champions League biyar a tarihi, yayin da PSG ta kai wasan karshe a bara, inda Bayern Munich ta yi nasara a kanta da ci 1-0.
Sai dai kuma rabonda Barcelona ta dauki Champions League tun kakar 2010/11.
Karawa tsakanin Barcelona da PSG:
Wasa tsakanin kungiyoyin biyu kan ja hankalin masu bibiyar tamaula, kuma a kakar 2017/18 Barcelona ta sha kashi da ci 4-0 a gidan PSG a Faransa.
A wasa na biyu ne da ake ganin Barcelona ta yi ban kwana da gasar, sai ta ci 6-1 ta kuma kai zagayen gaba.
Wasan yana daga cikin wanda za a dade ba a manta da shi ba a tarihi, koda yake Barcelona ce kan yi nasara a kan PSG idan suka hadu a gasar ta Zakarun Turai.
Sai dai a kakar 1994/95 PSG ce ta kai zagayen gaba a karawar da ta yi da Barcelona.
1994-95 Champions League Quarter Final
- Barca 1-1 PSG / PSG 2-1
(PSG ta kai zagayen gaba da ci 3-2)
1996-97 UEFA Cup Winners' Cup Final
- Barca 1-0 PSG
2012-13 Champions League Quarter Final
- PSG 2-2 Barca / Barca 1-1 PSG
(Barca ta kai zagayen gaba)
2014-15 Champions League Group F
- PSG 3-2 Barca / Barca 3-1 PSG
(Barca da PSG suka kai karawar zagayen gaba)
2014-15 Champions League Quarter Final
- PSG 1-3 Barca / Barca 2-0 PSG
(Barca ta kai karawar gaba da ci 5-1)
2016-17 Champions League zagaye na biyu
- PSG 4-0 Barca / Barca 6-1 PSG
(Barca ta kai karawar zagaye gaba da ci 6-5)

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan da suka buga kungiyoyin biyu:
Rafinha
Dan kwallon tawagar Brazil ya fara da koyon tamaula tun daga La Masia daga nan ya buga wa babbar kungiyar wasa 56 a tsakanin wasannin aro da ya yi a Celta da Inter Milan daga baya ya koma PSG a farkon kakar bana.
Mauro Icardi
Dan kwallonm Argentina ya buga wa matasan Barcelona tamaula 'yan shekara 18 da 19 tsakanin shekarar 2008 zuwa 2011 daga nan ya koma Sampdoria.
Neymar
Dan kwallon tawagar Brazil da zai buga wasan farko ba sakamakon jinya ya taka rawar gani a Barcelona inda ya yi wasa tare da Messi da kuma Luis Suarez.
A lokacin duk kungiyar da suka kama sai ta ji a jikinta, ko dai Messi ko Neymar ko Suarez wani sai ya ci kwallo ko biyu daga ciki, sannan kungiyar ta shafa leda.
A shekarar 2017 Neymar ya koma PSG da taka leda a matakin wanda aka saya mafi tsada a dunioya.









