Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ɗan Najeriya Kamaru Usman ya kafa tarihi a gasar UFC
An wallafa
Kamaru Usman ya ci gaba da zama a sawun farko a wasan UFC, bayan da ya yi nasara a kan Gilbert Burns, ya kuma kare kambunsa.
Usman mai shekara 33 ya yi wasa ne da dan kasar Brazil, wanda a baya suke atisaye tare.
Dan Najeriyar ya yi nasara ne a turmi na uku, inda ya yi wa mai shekara 34 bugun kwaf daya.
Kawo yanzu ya lashe dukkan wasa 13 da ya buga a gasar UFC, ya kuma doke tarihin Georges St-Pierre wanda ya ci karawa da yawa a ajin welterweight.
A baya can 'yan wasan na yin atisaye ne a Sanford MMA da ke Florida, daga baya Usman ya koma Elevation Fight Team a Colorado.