Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manchester City ta kafa tarihin cin wasa 15 a jere a dukkan fafatawa
Manchester City ta kai karawar dab da na kusa da na karshe wato Quarter finals a FA Cup bayan da ta doke Swansea 3-1 ranar Laraba.
City ta ci kwallayenta ta hannun Kyale Walker da Raheem Sterling da kuma Gabriel Jesus.
Ita kuwa Swansea City ta zare kwallo daya a wasan ta hannun Whittaker.
Wannan nasarar ta sa City ta yi wasa 15 a jere a dukan karawa ba tare da an doke ta ba.
Wadanda keda tarihin cin wasa 14 a jere a Ingila sun da Preston a kakar 1891-92 da bajintar da Arsenal ta yi a 1987-88.
Manchester City ta kai wasan Caraboa a bana, inda za ta fafata da Tottenham cikin watan Afirilu.
Kungiyar ta Etihad mai kwantan wasa daya tana jan ragamar teburin Premier League da tazarar maki biyar tsakaninta da Manchester United ta biyu.
Haka kuma City tana buga gasar Champions League, inda za ta buga fafatawar zagaye na biyu a wasan farko da Borussia Monchengladbach.
Saboda haka City na sa ran lashe Caraboa na bana da fa Cup da Premier League da kuma Champions League.