Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Europa League: An kai wasan Arsenal da United kasar Italiya
Manchester United da Arsenal za su buga wasanninsu da kungiyoyin Sifaniya a gasar Euopa League a Italiya.
Hakan ya faru ne saboda matakin da Sifaniya ta dauka na hana kungiyoyin kwallon kafa shiga kasar domin gudun yada cutar korona.
Sifaniya ta ce ba za ta bari kasashen da cutar korona ke yi wa ta'adi kawo yanzu su kai mata ziyara ba har da Birtaniya.
United da Real Socied za su buga karawar kungiyoyi 32 da suka rage a gasar a filin wasa na Juventus wato Allianz a Turin.
Shi kuwa wasan Arsenal da Benfica za su fafata a Stadio Olimpico a Rum.
Sai dai ba a sauya ranar da za su kara ba wato ranar Alhamis 18 ga watan Fabrairu.
United za ta karbi bakuncin karawa ta biyu ranar Alhamis 25 ga watan Fabrairu.
Sai dai ba a fayyace filin da Arsenal za ta kece raini da Benfica ba a wasa na biyu da za su kara ranar 25 ga watan nan.
Watakila wasan Champions League tsakanin Chelsea da Atletico Madrid a Sifaniya shi ma a sauya wurin da za su fafata a tsakaninsu.
Wasan Manchester City da na Liverpool da ya kamata su yi gumurzu da kungiyoyin Jamus an kai shi Hungary.
Itama Jamus ta hana mutane shiga kasarta musamman wadanda cutar korona ke kara tasiri a wurarensu har da Birtaniya.