Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Mbappe, Grealish, Barkley, Raphinha, Musa, Shawcross
Ɗan wasan gaba na Paris St-Germain Kylian Mbappe na iya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi da ƙungiyar gabanin komawarsa Real Madrid nan da shekara biyu mai zuwa, domin da alama Real ba ta da kuɗin da za ta ɗauki Mbappen. (AS - in Spanish)
Real Madrid ba za ta yin yuƙurin sayen Mbappe ba har sai PSG ta ta shirya yin haka. (Marca)
Aston Villa na shirin sabunta kwantiragin Jack Grealish mai shekara 25, kuma dan wasanta na tsakiya, za ta kuma inganta albashinsa. (90 Min)
Liverpool na sa ido kan Raphinha, dan wasan gefe dan kasar Brazil mai shekara 24 bayan da ya burge a wannan kakar wasan tare da Leeds United. (Football Insider)
West Bromwich Albion na kokarin samo kudin da za su dauki Ahmed Musa, dan Najeriya kuma dan wasan gaba mai shekara 28 da Brighton, Burnley, Southampton da CSKA Moscow ke sha'awar dauka. (Mail on Sunday)
Ɗan wasan baya na Ingila Ryan Shawcross mai shekara 33 na tattaunawa da Stoke City kan soke kwantiraginsa saboda ya sami damar komawa Inter Miami ta Amurka. (90 Min)
Celtic ta saka wata bukata a kwantiragin dan wasan baya Ben Davies daga Preston North End wanda zai ba Liverpool damar sayen dan wasan mai shekara 25 idan ta so yin haka. (Sunday Mirror)
Barcelona ba za ta amice da tayin kasa da euro miliyan 15 ba ga duk kungiyar da ke son daukan Neto Murara, wanda mai tsaron gida ne kuma mai shekara 31. (Marca)
Dan wasan baya dan asalin kasar Faransa William Saliba, mai shekara 19 ya sha wuya a Arsenal amma ya lashe gasar dan wasa mafi kwazo na wannan watan a Nice. (Metro)
Tsohon dan wasan tsakiya na Chelsea Michael Ballack ya ce "da alama Timo Werner na bukatar sauya salon wasansa" yayin da yake tattauna lamarin dan wasan mai shekara 24 wadanda suka hada da rashin zura kwallaye . (Omnisport, via Metro)