Premier League: Aston Villa ta doke Arsenal a wasan mako na 23

An wallafa

Minti biyu kacal da take wasa Aston Villa ta cilla wa Arsenal ƙwallo a zare a wasan mako na 23 na Premier League.

Tsohon mai tsaron ragar Arsenal ɗin ne, Emiliano Martinez, ya fara bugo ƙwallon wadda Bertrand Traore ya tsinta bayan Soares ya yi kuskure, inda shi kuma Ollie Watkins ya cilla ta zaren Mat Ryan.

Wannan ne karon farko da Villa ta yi nasara kan Arsenal a wasa biyu a jere cikin shekara 28.

Ranar 8 ga watan Nuwamban 2020 Villa ta casa Arsenal da 0-3 har gida a gasar Premier.

Tsohon golan na Arsenal ya hana Granit Xhaka farke ƙwallon ɗaya tilo a lokacin da ya ɗaɗa masa wani bugun tazara.

Da wannan sakamako, Villa ta zama ta takwas a teburi, yayin da Arsenal ke mataki na 10.