Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Huesca v Real Madrid: Zinedine Zidane ya nemi 'yan jarida su rika 'mutunta' shi
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya bukaci 'yan jarida su rika "mutunta" shi kuma ya ce har yanzu kungiyar tana fafatawa a gasar La Liga.
Real tana mataki na uku a teburin gasar, inda take bayan Atletico Madrid, wadda ke saman teburin da maki 10 amma ta fi ta yawan buga wasa.
Kuma yadda kungiyar ta gaza yin katabus a 'yan kwanakin nan ya sa kafafen watsa labari sun soma caccakar kocin dan kasar Faransa.
"Abin da yake ba ni dariya shi ne yadda kuke tambaya ta me ya sa nake fushi," in ji Zidane a taron manema labarai ranar Juma'a.
"Bai kamata 'yan jarida ku rika yi min abin da kuke yi min ba. Mun dauki kofi a kakar wasan da ta wuce don haka ina ganin ya kamata ku mutunta ni.
"Mun samu damar fafatawa a gasar La Liga a kakar wasan bana, akalla hakan ya sa muna cikin kakar wasa. A kakar wasa mai zuwa, akwai bukatar sauyi, amma a wannan shekarar ku bar mu, tawagar da ta dauki kofi a kakar wasan da ta gabata tana fafatawa a kakar wasa ta wannan shekarar ai.
"Ba wai mun shekara 10 ba ne (da daukar kofi), a kakar wasan da ta wuce ne. Akalla ya kamata ku mutunta mu kan abubuwan da muka samu nasara a kansu. Ku ('yan jarida) kun cika surutu. Me ya sa ba za ku kalle ni ido da ido ku gaya min cewa kuna so a kore ni daga kungiyar nan ba, ba a bayan idona ba."
An sake nada Zidane a matsayin kocin Real a watan Maris na 2019, bayan ya jagoranci kungiyar wajen daukar kofin Zakarun Turai sau uku a jere da kuma kofin lig a kakar 2016-17 lokacin shugabancinsa na farko.
Dan kasar Faransa mai shekara 48 zai jagoranci kungiyar a fafatawa da kungiyar da ke kasan teburin gasar La Liga Huesca ranar Asabar da misalin karfe (15:15 GMT) bayan Madrid ta sha kashi a hannu Levante kodayake bai halarci wasan ba saboda ya kamu da cutar korona
"An killace ni tsawon mako biyu, na matsu na fito na kuma nuna wa duniya cewa zan jajirce har zuwa karshe," in ji shi.
A wasan na yau, Sergio Ramos ba zai fafata ba saboda raunin da ya ji, a yayin da Zidane ya sanya masu tsaron raga uku a tawagarsa mai mutum 17.
Eden Hazard, Dani Carvajal, Federico Valverde, Rodrygo da Lucas Vazquez su ma ba za su shiga karawar ba saboda jinya, yayin da aka dakatar da Eder Militao.