Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gasar Australian Open za ta kyale ƴan kallo 30,000 a kowace rana
Za a kyale kimanin ƴan kallo 30,000 su hallara a filayen wasan kwallon Tennis na Gasar Austalian Open inji ministan wasanni na jihar Victoria.
An amince wa mutum 30,000 su bayyana a kowane yini amma cikin kwanaki takwas na farkon fara gasar, inda za a yi wasu wasannin da rana, wasu kuwa sai da dare za a yi su.
Daga na za a rage yawansu zuwa 25,000 daga matakin daf da kusa da na karshe na gasar - wanda rabin wadanda su ka hallara ke nan a shekarun baya.
Ana yin gasar Australian Open ne daga 8 - 21 ga watan Fabrairu a birnin Melbourne.
'Yan wasan da za su bayyana a Gasar ta Australian Open sun fara barin dakunan da aka killace su bayan da suka shafe kwana 14 saboda dokokin yakar annobar korona.
A farkon watan Janairu, fiye da ƴan wasa 1,700 tare da masu yi mu su hidima su ka isa ƙasar a jiragen sama na musamman da aka samar.
Yawancin ƴan wasan sun sami damar fita daga dakunansu domin yin wasnnin motsa jiki na tsawon sa'a biyar, amma akwai wasu ƴan wasan su 72 da aka killace dare da rana saboda an gano masu cutar korona acikin jiragen da su ka kai su ƙasar ta Australia.