Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo: 'Yan sanda na binciken dan wasan Juventus kan budurwarsa
'Yan sandan Italiya suna binciken dan kwallon Juventus Cristiano Ronaldo saboda zargin bulaguron da ya yi domin yin bikin ranar zagayowar haihuwar budurwarsa.
Ana zarginsa da karya dokar kullen Covid-19 saboda tafiyar da ya yi daga lardin Piedmont zuwa Valle d'Aosta.
Wani hoton da aka wallafa a shafin sada zumunta wanda daga bisan aka goge ya nuna shi da abokiyar zamansa a wani wajen shakatawa, a ranar da Georgina Rodriguez ta cika shekara 27 da haihuwa.
Daruruwan mutane ne ke mutuwa a Italiya yayin da dubbai suke kamuwa da cutar korona.
Cutar ta yi wa kasar illa sosai lokacin da ta barke a zagayen farko a shekarar da ta gabata kuma yanzu ta fada rikicin siyasa bayan ta yi yunkurin rage yaduwar cutar a karo na biyu.
'Yan sandan lardin Valle d'Aosta sun ce suna binciken mutanen biyu saboda balaguron da suka yi zuwa wurin shakatawa da wasan zamiya na Courmayeur.
Yanzu dokokin Italiya sun haramta mutanen da ke zaune a wuraren da cutar korona ta yi kamari tafiya zuwa wasu yankunan sai dai idan aiki ne zai kai su ko kuma suna da wan mazauni a can.
Rahotanni daga kafafen watsa labaran Italiya sun ce Ronaldo da abokiyar zaman nasa sun yi tafiyar ne ranar Talata inda suka kwana a otal din wurin shakatawar sannan suka koma Turin, birnin da kungiyar Ronaldo take da mazauni, ranar Laraba.
Rodriguez, wadda mai tallan kayan kawa ce, ta wallafa hotonsu suna bikin zagayowar ranar haihuwarta a gidansu a shafinta na sada zumunta inda take da mabiya fiye da miliyan 23.
Za a iya cin su tara idan aka same su da laifi.