Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar cinikin 'yan kwallo: Makomar Pogba, Rice, Wijnaldum, Garcia, Wilshere, Martinez, Neto
Juventus na shirin sake daukar dan wasan Manchester United Paul Pogba, mai shekara 27, a bazara idan Old Trafford ta rage farashin da ta sanya a kan dan wasan na Faransa, wanda kwangilarsa za ta kare a bazarar 2022. (Calciomercato, via Sunday Express)
Kocin West Ham David Moyes ya ce Chelsea da Manchester United ba su tuntubi kungiyar ba a game da yiwuwar daukar dan wasan tsakiya Declan Rice, mai shekara 22, bayan da aka yi ta rade-radin cewa suna zawarcin dan wasan na Ingila. (Amazon, via Mail on Sunday)
Kazalika Moyes ya ce West Ham ta nemi biyan 'yan wasanta "makudan kudi" amma ba su amince su karba ba. (Evening Standard)
Kwangilar dan wasan tsakiyar Netherlands Georginio Wijnaldum a Liverpool za ta kare a bazara kuma dan wasan mai shekara 30 ba zai sabunta zamansa ba domin yana son ya cika burinsa na tafiya Barcelona. (Sunday Mirror)
Ana hasashen cewa dan wasan Manchester City Eric Garcia, wanda kwangilarsa za ta kare a bazara, zai tafi Barcelona sai dai da alama daukar dan wasan na Sifaniya mai shekara 20 ba zai yiwu ba a watan Janairu bayan Nou Camp ta dage zaben shugabanta kasarta zuwa watan Maris. (Manchester Evening News)
Bournemouth za ta iya kulla yarjejeniya da tsohon dan wasan Arsenal da Ingila Jack Wilshere mai shekara 29. Dan wasan yana yin atisaye a kungiyar tun bayan da ya bar West Ham. (Talksport)
Borussia Dortmund na son daukar dan wasan PSV Eindhoven Donyell Malen, mai shekara 21, wanda ya taba murza leda a Arsenal, domin ya maye gurbin Jadon Sancho idan dan wasan na Ingila ya bar kungiyar. (Soccer News, via Daily Star on Sunday)
West Brom ta soma tattaunawa domin yiwuwar karbo aron dan wasan Celta Vigo da Turkiyya Okay Yokuslu, mai shekara 26, a yayin da take shirin dauko 'yan wasa uku a watan Janairun da muke ciki. (Mail on Sunday)
Da alama dan wasan Argentina mai shekara 23 Lautaro Martinez zai sabunta zamansa a Inter Milan. An yi hasashen cewa dan wasan zai tafi Barcelona a bazara, . (Sportweek, via Football Italia)
Kocin Barcelona Ronald Koeman ya ce kungiyar ta yi fatali da bukatar dan wasan Brazil Neto ta barin kungiyar, a yayin da ake rade radin cewa dan wasan mai shekara 31 zai tafi Arsenal. (Metro)