Kasuwar cinikin 'yan kwallon kafa: Makomar Rice, Tomori, Drinkwater, Garcia da Lacazette

An wallafa

Manchester United ta shirya fafatawa da Chelsea a fafutukar daukar dan wasan West Ham dan kasar Ingila Declan Rice, mai shekara 22, a bazara mai zuwa. (ESPN)

AC Milan tana son samun zabin sayen dan wasan Chelsea da Ingila Fikayo Tomori idan ta karbo aronsa a watan nan. Kungiyar ta Italiya za ta biya £26m kan dan wasan mai shekara 23. (Guardian)

Dan wasan Chelsea dan kasar Ingila Danny Drinkwater, mai shekara 30, yana daf da sanya hannu domin tafiya zaman aro a kungiyar Kasimpasa ta kasar Turkiyya, bayan ya yi ta fama a Stamford Bridge tun lokacin da aka saye shi daga Leicester a kan £35m a 2017. (Mail)

Pep Guardiola ya ce dan wasan Sifaniya Eric Garcia zai iya barin Manchester City idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallon kafa ta wannan wata na Janairu. Barcelona tana son daukar dan wasan mai shekara 20, wanda kwangilarsa za ta kare a bazarar nan. (Sky Sports)

Mutum uku da ke takarar shugabancin Barcelona sun amince a jinkirta zabe daga ranar 24 ga watan Janairu zuwa ranar 7 ga watan Maris bayan an kaddamar da sabbin dokokin yaki da Covid-19 a lardin. (AS)

Hakan na nufin watakila Barcelona ta jinkirta har sai kwangilar Garcia ta kare a bazara kafin ta dauke shi, yayin da kuma kungiyar ba za ta iya biyan kudin dauko tsohon dan wasan makarantar horas da 'yan kwallon nata ba a watan nan na Janairu. (Marca)

Bayern Munich ta tuntubi Real Madrid a game da daukar dan wasan Brazil Eder Militao, mai shekara 22, a matsayin wanza zai maye gurbin dan wasan Austria David Alaba, mai shekara 30, wanda ke dab da tafiya Madrid. (Goal)

Kocin Atletico Madrid Diego Simeone yana son daukar dan wasan Arsenal da Faransa Alexandre Lacazette, a yayin da dangataka ta yi tsami tsakanin dan wasan mai shekara 29 da kocin Arsenal Mikel Arteta. (AS - in Spanish)

Kungiyoyi uku na son daukar dan wasan Arsenal Folarin Balogun, mai shekara 19, a watan da muke ciki, kodayake kungiyar tana da kwarin gwiwa zai sabunta kwangilarsa. (Guardian)

Everton na son aron dan wasan Bayern Munich dan shekara 19 dan kasar Netherlands Joshua Zirkzee, tare da zabin sayensa baki daya. (Mail)