Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mesut Ozil: Dan wasan Arsenal na dab da tafiya Fenerbahce
- Marubuci, Daga Simon Stone
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
- An wallafa
Dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil ya kusa kammala kulla yarjejeniyar tafiya kungiyar kwallon kafar Fenerbahce da ke Turkiyya.
Har yanzu akwai sauran rabin kaka guda kafin wa'adin kwangilar dan wasan mai shekara 32 ta kare ta Arsenal sai dai dukkan bangarorin sun yi nisa a tattaunawa wadda ake sa ran za ta kai ga gintse kwangilar tasa.
Hakan zai ba shi damar tafiya Istanbul a kwanaki masu zuwa.
Arsenal ba ta sanya Ozil a tamaula ba tun wasan da suka doke West Ham da ci 1-0 a watan Maris kuma kocin kungiyar Mikel Arteta ya juya masa baya.
Ya koma Arsenal daga Real Madrid a kan £42.4m a shekarar 2013 inda ya taimaka mata wajen lashe kofunan FA sau uku.
Ozil ya bayyana shaukinsa na tafiya Fenerbahce a wani shirin tambaya da amsa da ya gudanar a shafukan sada zumunta a wannan makon.
Ya shaida wa mabiyansa cewa: "Fenerbahce kamar yadda Real Madrid da ke Spain take. Ita ce kungiya mafi girma a kasar."
Rahotannin da wasu kafafen watsa labaran Trukiyya suka bayar a farkon wata sun nuna cewa Fenerbahce za ta dauki Ozil a watan nan na Janairu.
An haifi Ozil a Jamus amma iyayensa 'yan asalin Turkiyya ne, kuma a baya shugaban Fenerbahce Ali Koc ya ce babban burinsu shi ne su dauki Ozil.
A 2019 kungiyar ta Turkiyya wadda sau 19 tana lashe kofin Super Lig ta ce ba za ta dauki Ozil ba saboda ba ta da kudi.
Kungiyar ta fada matsin tattalin arziki a shekarun baya bayan nan lamarin da ya bai wa kungiyar Istanbul Basaksehir damar lashe kofin a karon farko a watan Yulin da ya gabata.
Ozil ya murza leda a wasanni 10 tun bayan da aka nada Arteta a matsayin koci a watan Disamba na 2019, sai dai bai sake buga wasa ba tun da aka koma tamaula bayan dokar kullen farko sanadin barkewar annobar korona a watan Yuni.