Liverpool: Klopp ya ce babu inda Salah zai je

Asalin hoton, Getty Images
An wallafa
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya musanta zargin cewa ɗan wasansa Mohamed Salah ba ya jin daɗin murza leda a ƙungiyar.
Salah a kwanakin baya ya shaida wa wata jaridar Spain cewa bai ji daɗi ba kan yadda aka hanashi zama kyaftin ɗin Liverpool a wasansu da FC Midtjylland inda aka bai wa Trent-Alexander Arnold kambun kyaftin.
Ɗan kwallon Masar ɗin mai shekara 28, ya ƙi musanta cewa zai iya komawa Real Madrid ko Barcelona.
"Mo na cikin yanayi mai kyau kuma babu wata matsala," in ji Klopp.
Sallah ya zura ƙwallo 13 a kakar wasa ta bana a gasar Firemiya a yayin da Liverpool ke saman teburin gasar.







