Kasuwar 'yan ƙwallo: Korar Tuchel da PSG ta yi ya kawo wa Madrid cikas a sayen Mbappe

Kylian Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Sallamar da PSG ta yi wa kocinta Thomas Tuchel ta kawo wa yunƙurin Real Madrid cikas na sayen ɗan wasan gaban Faransa na ƙungiyar, Kylian Mbappe mai shekara 22 a ƙarshen kakar bana. (AS)

Atletico Madrid na duba yiwuwar karɓar ɗan wasan bayan Arsenal mai shekara 23 kuma ɗan Ingila, Ainsley Maitland-Niles, a matsayin aro a watan Janairu. (Mail)

Haka nan Atletico na son ɗaukar ɗan wasan bayan Chelsea Marcos Alonso yayin da ɗan ƙasar Spain ɗin mai shekara 29 ya kasa samun buga wasanni a kwanan nan. (El Chiringuito)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer na son sayen ɗan wasan baya zuwa tsakiya a shekara mai kamawa amma abu ne mai wuya ya nemi David Alaba na Bayern Munich, wanda kwantaraginsa zai ƙare a ƙarshen kakar bana. (Telegraph)

Kocin AC Milan Stefano Pioli na son ɗan wasan tsakiyar ƙasar Turkiyya Hakan Calhanoglu, wanda ake alaƙantawa da Man United ya ci gaba da zama a ƙungiyar yayin da ake tattaunawar bai wa ɗan shekara 26 ɗin sabon kwantaragi. (Goal)

Manchester City da Tottenham na saka wa mai shekara 29 ido na ƙungiyar Atalanta da Netherlands mai suna Marten de Roon. (90 Min)

Barcelona ta musanta rahotannin da ke cewa tana son ɗaukar ɗan wasan bayan Arsenal mai shekara 28 kuma ɗan Jamus, Shkodran Mustafi. (Mundo Deportivo)