An dakatar da Trippier mako 10 saboda karya dokar yin caca

Kieran Trippier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, England defender Kieran Trippier (left) has made 19 appearances for Atletico Madrid this season
An wallafa

An dakatar da dan wasan Atletico Madrid, Kieran Trippier daga shiga sabgobin tamaula har mako 10.

An kuma ci shi tarar fam 70,000 saboda hukumar kwallon kafa ta Ingila ta same shi da laifin karya dokar yin caca.

Dan kwallon tawagar Ingilan, mai shekara 30 ya musanta laifi bakwai da ake tuhumarsa.

Sai dai kuma an same shi da laifi hudu ƙarara a lokacin da ake ji ta bakinsa a lokacin tare da hukumar kwallon Ingila.

Ya aikata laifin ne a watan Yulin 2019, lokacin da dan kwallon ya koma Atletico daga Tottenham da taka leda.

Hukuncin dakatar da shi da aka yi ya fara aiki ne nan take.

Dan kwallon ba zai buga wa Atletico wasa 12 ba, har da na Champions League karawar zagaye na biyu da Chelsea ranar 23 ga watan Fabrairu.

Sai dai zai koma fagen fama a karawar hamayya a gasar La Liga tsakanin Real Madrid da Atletico Madrid ranar 7 ga watan Maris.