Rawar da Mbappe ya taka a PSG wadda ya ci wa kwallo na 100 ranar Asabar

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Asabar Paris St Germain ta doke Montpellier da ci 3-1 a gasar Fench Ligue 1 ranar Asabar.
Colin Dagba ne ya fara ci wa PSG kwallo, kuma na farko da ya yi wannan bajintar a kungiyar, bayan da ya samu tamaula daga wajen Angel di Maria.
Dan wasan Ingila, Stephy Mavididi mai shekara 22 shi ne ya farke kwallo, daga baya PSG ta zura na biyu a raga ta hannun Moise Keane.
Mbappe ne ya zura na uku kuma a raga kuma na 100 da ya ci wa Paris St Germain a wasa 137 da ya buga wa kungiyar.
Da wannan sakamakon PSG wacce ta buga wasa 13 a kakar bana a gasar Faransa tana ta daya da maki 28.
Dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 27, Mbappe shi ne na biyar a jerin wadanda suka ci wa PSG kwallo 100 ko fiye da hakan.
Wanda ke kan gaba shi ne Edinson Cavani mai 200 a raga sai Zlatan Ibrahimovic mai guda 156, sannan Pauleta da ya ci 109 da kuma Dominique Rocheteau wanda ya zura 100 a raga.
Mbappe ya ci kwallo 27 a kungiyar Monaco, kafin ya koma PSG da taka leda kan fam miliyan 165.
Dan wasan wanda ya lashe kofin duniya a Rasha ya ci kwallo 78 da kafar dama da 20 da kafar hagu da kuma biyu da ka a PSG.
Jerin wadanda ke kan gaba a ci wa Pris St Germain kwallaye a raga kawo yanzu:
1. Edinson Cavani: 200 goals
2. Zlatan Ibrahimovic: 156 goals
3. Pedro Miguel Pauleta: 109 goals
4. Kylian Mbappé, Dominique Rocheteau: 100 goals
6. Mustapha Dahleb: 98 goals
7. François M'Pelé: 95 goals
8. Angel Di Maria, Safet Susic: 85 goals
10. Neymar Jr: 76 goals












