Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Neymar, Aouar, Dembele, Haaland, Gimenez, Gray

Asalin hoton, Getty Images
Dan takarar mukamin shugaban kungiyar Barcelona Emili Rousaud ya ce idan aka zabe shi, zai sayo 'yan wasa "biyu, cikinsu akwai Neymar", dan wasan gaba na kasar Brazil da ya bar Barca zuwa Paris St Germain a 2017. (Marca - in Spanish)
Lyon ta hakura da saka Houssem Aouar wanda Arsenal ke nema ruwa a jallo domin ya buga ma ta wasa ranar Lahadi da kungiyar Riems saboda dan Faransar mai shekara 22 ya ki shiga fili bayan da kocinsa ya bukaci ya sanya jesi a wasan da suka lallasa Angers. (L'Equipe via Mirror)
Manchester United ba ta fasa neman Ousmane Dembele daga Barcelona ba amma za su za su iya amincewa ya tafi can a matsayin dan aro. Shekarar Dembele 23. (Sport - in Spanish)
Babban shugaban kungiyar Borussia Dortmund Michael Zorc na gani dan wasansu Erling Braut Haaland zai dade a kungiyar a lokaci mai tsawo sosai, duk da cewa Real Madrid na sha'awar sayen dan wasan mai shekara 20. (Goal)
Chelsea na sha'awar sayo Jose Gimenez, dan wasan Atletico Madrid da Uruguay mai shekara 25. (Sun)
Tottenham na daf da sayo Demarai Gray daga Leicester. Dan wasan Ingilan mai shekara 24 zai kasance ba shi da kungiya daga watan Janairu. (Express)
Liverpool na iya samun fam miliyan 30 a watan Janairu idan ta sayar da dan wasanta Xherdan Shaqiri dan kasar Switzerlan mai shekara 29, da kuma Divock Origi mai shekara 25 wanda shi dan kasar Belgium ne. (Express)
Barcelona na iya kai samame domin sayo Sadio Mane dan wasa mai shekara 28 dan Liverpool ko kuma Gini Wijnaldum mai shekara 30, bayan da kwantiragin ci gaba da zaman Philippe Coutinho a Nou Camp ya kare. Da Barca ta bukaci wani dan wasan Liverpool da sai sun biya ta karin fam miliyan 89. (Star)
Golan Italiya Gianluigi Donnarumma mai shekara 21 na daf da sanya hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da buga was a kungiyarsa ta AC Milan. (Calciomercato - in Italian)
Manchester United ta yi wa Timothy Fosu-Mensah, dan wasanta mai shekara 22 dan kasar Netherlands sabuwar kwantiragi da zarar nasa ya kare a watan Janairu. (Manchester Evening News)











