Diego Maradona: Napoli za ta saka wa filin wasanta sunan shahararren ɗan wasan duniya

Asalin hoton, Getty Images
Napoli za ta yi alhini na musamman kan mutuwar shahararren dan wasan kwallon kafar duniya Diego Maradona.
Anjima kadan ne Napoli za ta buga wasan Europa League da kulob din HNK Rijeka.
A ranar Laraba ne Maradona ya mutu sakamakon bugun zuciya mako biyu bayan an yi masa tiyata a kwakwalwa.
A sanarwar da mamallakin kungiyar Aurelio de Laurentiis ya fitar, ya ce za a canza wa filin wasan Napoli suna daga Stadio San Paolo zuwa Stadio Diego Armando Maradona.
Haka ma magoya bayan kungiyar za su yi jimami na musamman a filin wasan, tare da goyon bayan mai garin Naples Luigi de Magistris.

Asalin hoton, Getty Images
Bugu da kari za a yi shiru na minti daya kafin fara wasan na daren yau.
A cewar mai garin Naples Luigi de Magistris: "Ina ganin sauya sunan San Paolo zuwa sunan ka abu ne da yakamata mu yi, don kafa shaida kan irin turbar da ka dora kungiyarmu a kai".
Mai garin ya kara da cewa "mun gode Diego. Za ka ci gaba da kasancewa tare da mu har abada.'

Asalin hoton, Getty Images
Maradona ya ci wa Napoli kofunan Serie A a shekarun 1987 da kuma 1990.
Kazalika ya ci wa kungiyar da ke birnin Naples kofin Zakarun Turai a 1989.











