Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Inter Milan na zawarcin Kante, Bayern Munich na son ɗauko 'yan wasan tsakiya
Inter Milan na duba yiwuwar dauko dan wasan Chelsea da Faransa N'Golo Kante a bazara inda The Blues ke shirye domin jin tayin da za a yi kan dan wasan mai shekara 29. (Gazzetta dello Sport, via Metro)
Zenit St Petersburg ta bayyana sha'awar dauko dan wasan Liverpool da Croatia Dejan Lovren, mai shekara 31. (Liverpool Echo)
AC Milan na son dauko dan wasan Real Madrid da Serbia Luka Jovic, mai shekara 22, wanda Leicester City da Arsenal suke zawarci. (Calciomercato, via Leicester Mercury)
Kai Havertz yana son barin Bayer Leverkusen saboda sun gaza samun gurbin gasar Zakarun Turai don haka akwai bukatar Chelsea ta nuna wa dan wasan na Jamus mai shekara 21 cewa za ta iya samun gurbin zuwa gasar Zakarun Turai kafin ya amince ya koma can. (Bild)
Bayern Munich na kuma sha'awar dauko 'yan wasan Faransa biyu da ke buga gasar Firimiya - dan wasan Tottenham Tanguy Ndombele, mai shekara 23, da kuma dan wasan Chelsea Tiemoue Bakayoko, mai shekara 25. (Le10Sport, in French)
Dan wasan Swedin Zlatan Ibrahimovic, mai shekara 38, ya ce ba shi da tabbas kan makomarsa a AC Milan ganin cewa babu wata tartibiyar magana game da kwangilarsa kasa da wata daya kafin ta kare. (Sky Sports)
An kyale 'yan kallo kusan 5,000 sun shiga filin wasa don kallon fafatawar farko a wasan zumunci da Paris St-Germain ta yi inda ta doke Le Havre da ci 9-0. (France 24)