Dortmund na son sayar da Sancho kan euro 130m, Barcelona ta haƙura da Neymar

An wallafa

Borussia Dortmund ba za ta karbi kasa da euro 130m kan dan wasan Ingila Jadon Sancho, 20, wanda rahotanni ke cewa zai koma Manchester United, ba. (Westdeutsche Allgemeine Zeitung, via Manchester Evening News)

Dan wasan Senegal Kalidou Koulibaly, mai shekara 29, ya ce zai iya kammala sana'arsa ta tamaula a Napoli, duk da rahotannin da ke cewa yana son komawa Liverpool, Manchester City, Manchester United koReal Madrid. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

Barcelona ta karaya a yunkurin da take yi na komo da dan wasan Paris St-Germain da Brazil Neymar, mai shekara 28, Nou Camp a bazarar nan. (Marca)

Leicester tana son dauko dan wasan Serbia Luka Jovic, mai shekara 22, daga Real Madrid a kan £31m domin ta hada shi da Jamie Vardy a kakar wasa mai zuwa. (Mail on Sunday)

Su maAC Milan daChelsea suna son dauko Jovic. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Bristol City tana son dauko kocin Rangers Steven Gerrard domin ya maye gurbin kocin da ta kora daga aiki Lee Johnson. (Sunday Express)

Juventus da Manchester City sun bi sahun Liverpool a fafutukar dauko dan wasan Bayern Munich da Sufaniya Thiago Alcantara, mai shekara 29. (Tuttomercatoweb - in Italian)

Chelsea da Inter Milan sun soma tattaunawa da Lille domin yiwuwar dauko dan wasan Faransa Jonathan Ikone, mai shekara 22. (Le 10 Sport - in French)

Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce ba shi da tabbaci kan ko dan wasan Colombia James Rodriguez, mai shekara 28, zai sake buga wasa a kungiyar. (AS)

Juventus da Inter Milan suna son dauko dan wasan Roma da Italiya Nicolo Zaniolo, mai shekara 21, a bazarar nan.(Tuttosport - in Italian)

DoleBarcelona ta biya euro 20m ga tsohuwar kungiyar Ousmane DembeleBorussia Dortmund idan suka sayar da dan wasan na Faransa mai shekara 23 a bazarar nan. (Bild - in German)

Sabon kocin Real Betis Manuel Pellegrini yana son karbo aron dan wasan Real Madrid Brahim Diaz, mai shekara 20, a kakar wasa mai zuwa. Pellegrini ya yi aiki da Diaz a Malaga kuma shi ne ya bai tsohuwar kungiyarsa Manchester City shawarar daukar dan wasan na Sufaniya. (Mundo Deportivo - in Spanish)

Chelsea ta bi sahun Manchester City da Juventus domin bibiyardan wasan Penarol dan shekara 18Facundo Pellistri. (Calciomercato - in Italian)

Dan wasanFlamengo mai shekara 23 dan kasar Brazil Gerson, wanda ake rade radin cewa zai koma Chelsea da Tottenham, ya ce ba shi da niyyar barin kungiyarsa. (Globo Esporte - in Portuguese)