An shirya ci gaba da wasannin Bundesliga daga ranar 9 ga watan Mayu

The last Bundesliga match, Borussia Monchengladbach v Cologne on 11 March, was played behind closed doors

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wasan Borussia Monchengladbach da Cologne ranar 11 ga Maris shi ne na karshe da aka yi ba tare da 'yan kallo ba
An wallafa

Bayan da aka dakatar da wasanni a duniya don gudun yada cutar korona, an kagu a ci gaba da gasar Bundesliga a watan Mayu don karkare kakar bana ba tare da 'yan kallo ba.

Jamus na kan gaba wajen dakile annobar, bayan da ta gwada mutane da yawa tun farkon bullar cutar wanda hakan ya sa kasar ta zama daga cikin kasashen duniya da ke da karancin mutanen da suka kamu da annobar da wadanda ta hallaka.

Mahukuntan da ke gudanar da gasar Jamus ne keda alhakin karkare wasannin Bundesliga da wasa ta kasa da ita a daraja don kammala kakar bana.

Ranar Alhamis kungiyoyi 36 da ke buga wasannin suka zauna taro da muhukunta kwallon kafar kasar suka kuma cimma yarjejeniyar ci gaba da wasannin daga ranar 9 ga watan Maris.

Sai dai mahukunta kwallon kafar kasar za su amsa tambayoyi masu tsauri dangane da hujjar ci gaba da gasar kafin a amince su koma fagen fama ba tare da 'yan kallo ba.