Mai kuke son sani kan karawar El Clasico?

El Clasico

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Barcelona a wasan mako na 26 a gasar La Liga da za su kara a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.

Wannan ne wasa na biyu da kungiyoyin za su kece raini a fafatawar hamayya da ake kira El Clasico.

A ranar 18 ga watan Disambar 2019, kungiyoyin biyu suka tashi wasa 0-0 a Camp Nou.

Duk wadda wadda ta samu nasara a wasan yau za ta koma ta daya a kan teburin La Liga a makon nan.

Yanzu dai Barcelona ce ke kan gaba da maki 55, sai Real Madrid ta biyu da maki 53.

Kocin Real Madrid ya bayya sunayen 'Yan wasa 19 da za su kara da Barcelona a Santiago Bernabea.

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Toni Fuidias.

Masu tsaron baya: Carvajal, Militao da Ramos da Varane da Marcelo da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da kuma Isco.

Masu buga gaba: Benzema da Bale da Lucas Vazquez da Mariano da kuma Vinicius Jr.

Jordi Alba yana daga cikin 'yan wasan da za su buga wa Barcelona El Clasico ranar Lahadi a gidan Madrid.

Mai tsaron bayan ya yi jinya ne da bai yi wa Barca wasa biyu baya ba.

Shima Gerard Pique na cikin 'yan wasan Barcelona da zai buga wasan na hamayya, bayan da a baya ake cewar da kyar ne idan zai buga fafatawar.

Bayan da 'yan wasa Luis Suarez da Ousmane Dembele da kuma Sergi Roberto ke jinya, hakan ne ya bai wa matasa Ansu Fati da kuma Alex Collado damar shiga cikin 'yan wasan Barca.

'Yan wasan Barcelona 18 da aka je da su Real Madrid.

Marc-Andre ter Stegen da Neto da Nelson Semedo da Gerard Pique da Samuel Umtiti da Clement Lenglet da Junior Firpo da kuma Jordi Alba.

Sauran sun hada da Sergio Busquets da Frenkie de Jong da Arthur Melo da Arturo Vidal da Ivan Rakitic da Alex Collado da Ansu Fati da Lionel Messi da Antoine Griezmann da kuma Martin Braithwaite.