Premier League: Man City ta yi canjaras da Crystal Palace

Crystal Palace

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Yunkurin Manchester City na daukar kofin Premier ya sake samun tasgaro yayin da Fernandinho ya ci gidansu a mintinan karshe a filin wasa na Etihad.

Kwallo biyu da Sergio Aguero ya ci sun tayar wa da Crystal Palace hankali bayan Cenk Tosun ya taimaka masu samun kwallo tun kafin hutun rabin lokaci.

Sai dai Palace din ne suka samu dama ta karshe bayan Wilfred Zaha ya yi kwance-kwance ya shararo kwallo cikin raga, inda Fernandinho ya dirka ta cikin ragarsu kafin Connor Wickham ya kai gare ta.

Canjaras din ya bar Man City maki 13 a kasan jagorar teburin Premier wato Liverpool, wadda ke da wasa biyu a hannu - za ta buga daya a gobe Lahadi tsakaninta da Manchester United da karfe 4:30.

Duk da irin shafa kwallo da Man City ta yi a wasan ba ta iya samun wata damar cin kwallo ta kai-tsaye ba.