Real Madrid ta haye saman teburin La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Casemiro ne ya ci kwallo biyu
An wallafa

Real Madrid ta doke Sevilla a wasan La Liga mako na 20 a filin wasa na Santiago Bernebeu kuma ta dare saman teburi.

Casemiro ne ya ci kwallo har biyu, wadanda suka bai wa Madrid wannan nasara bayan VAR ta hana kwallon da Luuk de Jong ya ci a minti na 29.

Minti 12 da dawowa daga hutun rabin lokaci Casemiro ya ci ta farko sannan, inda de Jong ya sake farke ta.

Casemiro ya kara ta biyu a minti na 69 kafin a ba shi katin gargadi a minti na 88.

Wannan sakamakon ya sa Madrid ta haye saman tenburin La Liga da maki uku kafin Barcelona ta fafata da Granada a gobe Lahadi.