Ballon d'Or: Shin yanzu Ronaldo na iya ja da Messi?

    • Marubuci, Awwal Ahmad Janyau
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja
  • An wallafa

Kyautar gwarzon dan wasan duniya ta Ballon d'Or ta dade tana tasiri ga tsamar da ke tsakanin Messi da Ronaldo, zaratan 'yan kwallon duniya guda biyu.

Ana ganin ba a taba zaratan 'yan kwallo ba kamar Messi da Ronaldo a duniyar tamola wadanda suka shafe shekaru suna cin kwallaye da lashe kofuna a kungiyoyinsu.

Ronaldo da Messi sun shafe shekaru 10 suna raba wa juna kyautar gwarzon dan wasan duniya a tsakaninsu. Kuma sau biyar suna take wa juna baya a matsayin na biyu tun 2007.

Sai a 2018 ne Luka Modric ya ratso tsakaninsu ya lashe kyautar, kafin a bana Messi ya dawo ya karbi kyautar a karo na shida.

Messi ya doke babban abokin hamayyarsa Cristiano Ronaldo wanda ya zo a matsayi na uku bayan Virgil van Dijk na Liverpool.

Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya ne duk da bai lashe kofin zakarun Turai ba. Amma ya zira kwallaye 51 a wasanni 50 a kakar da ta gabata, tare da lashe wa Barcelona kofin La liga.

Bayar da Kyautar 2019 ga Messi ya kara farfado da muhawarar da aka dade ana yi kan wanda ya fi iya taka leda tsakanin Messi da Ronaldo.

Tun tafiyar Ronaldo zuwa Juventus daga Real Madrid, wasu suka fara tunanin hamayya tsakanin shi da Messi na Barcelona ta kawo karshe.

Amma yadda Ronaldo ya zo matsayi na uku, wata alama ce da ke nuna cewa har yanzu 'yan wasan biyu da suka haura shekara 30 suna kan ganiyarsu.

Ronaldo mai shekara 34, da Messi mai shekara 32, yadda suke taka leda ga alama har yanzu suna da sauran shekarun da za su ci gaba jan zarensu.

Wasu na ganin kyautar 2019 da Messi ya lashe zai iya zaburar da Ronaldo wanda ke taka leda a Juventus ga yakin sake lashe kyautar a badi.

Ronaldo Kafin ya koma Juventus, a tarinhinsa ya ci kwallaye 658 a wasanni 915, inda ya ci wa Real Madrid kwallaye 450 a wasanni 438

A Kakarsa ta farko ya ci wa Juventus kwallaye 28 a dukkanin wasannin da ya buga, kuma a kakar 2019-2010, dan wasan yanzu ya ci kwallaye bakwai.

Sannan a bana ya ci wa Portugal kwallaye 10.

Me Messi ya ce game da Ronaldo?

Messi ya ce ya yi hassadar Ronaldo a kaka biyu a jere yana lashe kyautar.

Ronaldo ya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya a shekarar 2016 da 2017 wanda ya ba shi damar kamo Messi da yawan kyautar sau biyar.

Messi ya ce ya fi son a ce shi kadai ya taba lashe kyautar sau biyar, kamar yadda ya shaidawa mujallar Faransa da ke bayar da kyautar Ballon d'Or.

"Na ji zafin lokacin da Ronaldo ya kamo ni, domin hakan ya nuna ba ni na fi kowa ba."

Ya ce Ronaldo ya lashe kyautar ne saboda Real Madrid ta lashe kofin zakarun Turai.

Da aka tambayi Messi game da dan kwallon duniya da ba a taba gani ba a tarihin tamaula, sai ya ce "Gaskiya ban sani ba."

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi an dauke su a matsayin manyan zaratan 'yan kwallo kafa biyu da ba a taba yi ba a duniya ba wai kawai a zamaninsu ba.

Messi da Ronaldo sun lashe jimillar kofi 63, wadanda ake ganin sun fi kowa yawan lashe kofi.