Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 17/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 17 ga watan Yuni 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Akwai yiwuwar Trump da shugaban Iran da kansu za su sanya hannu kan yarjejeniya

    Akwai yiwuwar shugabannin ƙasashen Iran da Amurka, Masoud Pezeshkian da Donald Trump, da kansu za su sanya hannu kan yarjejeniya domin kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakanin ƙasashen biyu a ranar Juma'a.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya ruwaito mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmail Baghaei, na bayyana cewa an tattauna batun kuma har yanzu ana ci gaba da nazarinsa.

    Kalaman nasa na zuwa ne bayan da Trump ya bayyana a wani taron manema labarai bayan taron ƙasashen G7 a Faransa cewa "wataƙila" zai halarci taron sanya hannu kan yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin tsakanin Amurka da Iran.

    Ana sa ran za a gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar tsakanin Iran da Amurka ne a garin Bürgenstock da ke ƙasar Switzerland ranar Juma'a.

  2. Trump ya ce wataƙila da kansa zai halarci zaman sanya hannu kan yarjejeniya da Iran

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce akwai yiwuwar ya halarci taron sanya hannu kan yarjejeniya da Iran, wanda aka shirya gudanarwa a ƙasar Switzerland a ranar Juma'a.

    A taron manema labarai bayan taron ƙasashen G7 da aka gudanar a Faransa, Trump ya yi watsi da rahotannin wasu kafafen yaɗa labarai na Amurka da ke cewa Iran za ta samu dala biliyan 300 domin sake gina ƙasar a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin.

    Ya bayyana rahotannin a matsayin "labaran ƙarya", yana mai cewa, "Ba za mu ba su kuɗi ba. Ba za mu ba su ko sisin kwabo daga cikin waɗannan kuɗaɗen ba."

    A ƙarshen taron manema labaran, an tambayi Trump ko zai ci gaba da zama a Turai domin halartar taron sanya hannu kan yarjejeniyar da Iran. Sai ya amsa da cewa, "Wataƙila."

    Daga nan sai ya yi barkwanci da cewa idan yarjejeniyar ba ta yi nasara ba, zai iya ɗora laifin hakan kan mataimakinsa, J. D. Vance.

  3. In da yaƙin Iran ya yi tsawo da an faɗa cikin bala'i - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce da yaƙin da Amurka da Isra'ila suka yi da Iran ya ɗauki lokaci mai tsawo, da duniya ta fuskanci mummunar matsalar tattalin arziki.

    Trump ya bayyana hakan ne a ƙarshen taron ƙasashen G7, inda ya ce an riga an cimma yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin, kuma ana sa ran sanya hannu a kanta a hukumance tun daga ranar Alhamis.

    Ya bayyana yarjejeniyar a matsayin wata nasara ga Amurka, yana mai cewa ta taimaka wajen kauce wa illolin da za su iya biyo bayan ci gaba da rikicin.

    Sai dai shugaban ya bayyana cewa akwai yiwuwar tattalin arzikin duniya ya shiga cikin wani "babban bala'i" in da ace yaƙin ya ci gaba da tsananta.

    Trump ya kuma ce yarjejeniyar ta ƙunshi alkawarin cewa Iran ba za ta ƙera ko mallakar makamin nukiliya ba.

    Tehran ta taɓa yin irin wannan alƙawari a wata yarjejeniya da aka cimma a lokacin mulkin tsohon shugaban Amurka, Barack Obama.

  4. An yanke wa wanda ya kashe ƴanmata takwas hukuncin ɗauri

    Wata kotu a ƙasar Amurka ta yanke wa wani da aka bayyana a matsayin ƙasurgumin mai kisan kai, Rex Heuerman, hukuncin ɗaurin rai da rai ba tare da damar neman afuwa ko sakin wucin gadi ba.

    Heuerman ya amsa laifin kashe wasu mata matasa takwas tsakanin 1993 zuwa 2010.

    An fi saninsa da suna "Gilgo Beach Killer" saboda an gano galibin gawarwakin waɗanda ya kashe a yankin Gilgo Beach da ke kusa da birnin New York.

    Rahotanni sun ce jami'ai sun shafe sama da shekara goma suna ƙoƙarin gano wanda ya aikata laifukan kafin daga bisani su samu nasara a binciken.

    An fara gano alaƙarsa da kisan ne bayan masu bincike sun samu lambar wata mota kirar akori-kura a ɗaya daga cikin wuraren da aka aikata laifin.

    Sai dai muhimmiyar hujjar da ta taimaka wajen kama shi ita ce gwajin ƙwayoyin halitta (DNA), bayan da aka auna samfurin da aka samu a jikin ɗaya daga cikin waɗanda aka kashe.

  5. Kotu a Birtaniya ta wanke Diezani daga laifukan rashawa

    Wata kotu da ke birnin London na ƙasar Birtaniya ta wanke tsohuwar Ministar albarkatun mai ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga zarge-zargen rashawa da ake yi mata.

    An zargi Diezani da karɓar cin hanci daga wasu shugabannin kamfanonin mai ta hanyar kayayyaki masu tsada da aka saya daga babban shagon Harrods, da gidaje masu tsadar miliyoyin daloli, da kuma sharholiya a jiragen sama masu zaman kansu.

    Sai dai bayan sauraron shari'ar, kotun ta yanke hukuncin wanke ta daga zarge-zargen da ake mata.

    Diezani ta riƙe muƙamin Minista a Najeriya tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015, a lokacin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.

    Haka kuma kotun ta wanke wasu mutum biyu da ake tuhuma tare da ita, wato ɗan'uwanta, Doye Agama, wanda babban limamin cocin Pentecostal ne, da kuma wata attajira a harkar mai, Olatimbo Ayinde.

    Hukuncin na zuwa ne bayan shafe shekaru ana gudanar da bincike da shari'a kan zarge-zargen da suka shafi cin hanci da rashawa da aka danganta da tsohuwar ministar.

  6. An yanke wa mutum 150 hukunci kan zargin da "ta'addanci" a Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta ce an yanke wa mutum 150 hukunci daga cikin 600 da ake zargi da ayyukan ta'addanci a ƙasar.

    Babban lauyan gwamnatin ƙasar Lateef Fagbemi ya shaida wa ƴan jarida cewa an saurari shari'o'i na mutum kusan 300 cikin kwanaki biyu.

    Ministan Shari'a Lateef Fagbemi, ya ce an fara zaman shari'un ne daga ranar Litinin zuwa Talata, inda ake sa ran ƙarin wasu mutum 84 da ake zargi za su gurfana a gaban kotu a ranar Laraba.

    Ɗaya daga cikin waɗanda aka yankewa hukunci shi ne Ali Mustapha, wani manomi mai shekaru 55 daga Jihar Borno, wanda kotun ta yanke wa hukuncin ɗaurin shekaru 15 ba tare da zaɓin tara ba, bayan ta same shi da laifin ɓoye bayanai kan ayyukan ƙungiyar Boko Haram a ƙauyensu na Katara.

    Haka kuma kotun ta yanke wa Isa Isiaka, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari saboda kin sanar da gwamnati bayanan da ya sani game da ayyukan ƙungiyar Boko Haram.

    Ana gudanar da shari'un ne ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, tare da sa ido daga masu lura da shari'a na cikin gida da na ƙasashen waje, ciki har da ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar NBA da hukumar kare haƙƙin ɗan adam.

    A cewar gwamnati, daga cikin shari'u 508 da suka shafi ta'addanci da aka gabatar a watan Afrilu, an samu hukunci kan mutum 386, inda aka yanke musu hukuncin ɗauri daga shekaru biyar zuwa ɗaurin rai da rai.

    An mayar da zaman shari'un daga Kainji da ke Jihar Neja zuwa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja. Fagbemi ya ce gwamnatin tarayya ta kuduri aniyar murkushe ta'addanci da duk wasu ayyukan da ke da alaƙa da shi a faɗin ƙasar.

    Rahotanni sun ce tun daga shekarar 2017, an yanke hukuncin dauri kan ɗaruruwan masu laifukan da suka shafi ta'addanci. Kafin waɗannan shari'u da ake gudanarwa, hukumomin ƙasar sun ce tuni aka ɗaure sama da mutum 700 kan laifukan ta'addanci.

  7. 'Kasuwar hannun jarin mai a ƙasashen turai sun yi faduwar da ba su taɓa yi ba'

    Hukumar kula da makamashi ta duniya ta ce kasuwar hannun jari ta mai a ƙasashen turai dake cikin ƙasashen OECD sun yi faduwar da ba su taba yi ba tun shekarar Alif dari tara da casa'in.

    A cikin rahotonta na baya-bayan nan na wata-wata, hukumar ta IEA ta ce, sannu a hankali kasuwar man fetur ta duniya za ta farfado daga matsalar da rufe mashigar Hormuz ta jefa ta, idan har aka kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

    Hukumar ta ce yaƙin Amurka da Iran ya haifar da gagarumin cikas a kasuwar mai ta duniya.

  8. Za mu ci gaba da kai wa Iran hare‑hare idan ta saɓa yarjejeniya - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ke Faransa domin halartar taron G7, ya bayyana cewa har yanzu ba a kammala cimma yarjejeniya da Iran ba yana mai gargadin cewa Amurka za ta ci gaba da kai wa Ira ɗin hari idan ta saɓa yarjejeniya kuma idan bai gamsu da yadda ake aiwatar da ita ba.

    Trump ya ce wannan yarjejeniya a halin yanzu “takardar fahimta ce kawai,” yana mai ƙara da cewa idan bai gamsu da sakamakon ba, za su koma kai hari kai tsaye.

    Yayin da ake jiran martanin Iran kan kalaman Trump, shugaban na Amurka ya ƙara da cewa ƙasarsa ba za ta zuba jari a Iran ba idan bai gamsu da yadda tafiyar da batun yarjejeniyar ba.

    Ya ce: “Idan ba na son yadda harkar yarjejeniyar ke tafiya, za mu sake harba makamai mu jefa musu bama‑bamai.”

    Ya kuma jaddada cewa idan Iran ba ta nuna “kyakyawar hali” wajen bin ƙa’idodin yarjejeniyar ba, Amurka za ta ɗauki matakin soja ba tare da jinkiri ba, lamarin da zai iya ƙara dagula yanayin tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Bugu da ƙari, Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar ba ta ƙunshi dage takunkumin da aka kakaba wa Iran nan take ba, yana mai cewa zai bayar da karin bayani kan wannan bangare a nan gaba.

  9. Mun ceto mutum biyar da aka sace a Kogi - Sojojin Najeriya

    Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun samu nasarar ceto mutum biyar da aka sace a jihar Kogi, yayin da waɗanda suke yi garkuwa da su suka tsere sakamakon hare-haren soji da ake ci gaba da kai musu.

    An samu wannan nasara ne a ranar 17 ga watan Yuni 2026, yayin da sojojin ke ƙara zafafa kai hare-hare kan maɓoyar ‘yan ta’adda a cikin dazukan jihar.

    A wani samamen toshe hanyoyi da aka gudanar daga sansanin sojin Oshokoshoko zuwa hanyar Adankolo ne sojojin suka gano mutanen da aka sace bayan da maharan suka yi watsi da su suna tserewa.

    Rahotanni na farko sun nuna cewa mutanen sun samu ‘yancinsu ne bayan da sojojin suka tilasta maharan tarwatsewa sakamakon hare-haren sama da ƙasa da aka kai musu.

    Daga nan ne aka kwashe su zuwa wurin da ke da tsaro, sannan aka kai su cibiyar lafiya ta soji domin ci gaba da kula da su.

    Rundunar sojin ta ce ana ci gaba da tattara bayanan sirri daga hannun wadanda aka ceto domin taimakawa wajen gano sauran ‘yan ta’addar da ke aiki a yankin, tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da matsa musu lamba har sai an murƙushe dukkan sansaninsu.

  10. Rasha ta buƙaci Isra’ila ta mutunta yarjejeniyar Iran da Amurka

    Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya buƙaci Isra’ila da ta mutunta yarjejeniyar fahimta tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana goyon bayan ƙasarsa ga duk wani mataki da zai rage tashin hankali a yankin.

    Lavrov ya ce Rasha na maraba da duk wata yarjejeniya da za ta kawo sauƙi a rikice-rikicen yankin, yana mai ganin hakan a matsayin mataki na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

    A cewarsa, yana da matuƙar muhimmanci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su cika ƙa’idojin yarjejeniyar, yana mai cewa bai dace ba wasu ƙasashe su bi dokoki, yayin da wasu ke kaucewa.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ta kai hare-hare a wasu wurare a kudancin Lebanon, yayin da Iran ke cewa dakatar da yaƙin Lebanon na daga cikin abubuwan da yarjejeniyar fahimta tsakaninta da Amurka ta ƙunsa.

  11. Me ya janyo musayar yawu tsakanin Rarara da Davido?

    Wata cece-ku-ce ta ɓarke a shafukan sada zumunta tsakanin fitattun mawaƙan Najeriya biyu Davido da Rarara.

    A ranar Talata da daddare ne dai fitaccen mawaƙin siyasa a arewacin Najeriya, Dauda Kahutu Rarara ya wallafa wani bidiyo a shafukansa na sada zumunta, inda a ciki ya soki fitaccen mawaƙin Kudancin ƙasar David Adedeji Adeleke da aka fi sani da Davido.

    Davido dai ya bayyana ne a wani bidiyon waƙa da ya gudanar a bikin shirye-shiryen fara gasar Kofin Duniya, sanye da riga mai ɗauke da tutar Najeriya rubuce da sunayen yara ɗaliban da aka sace a jihar Oyo.

    A watan da ya gabata ne dai wasu mahara masu iƙirarin jihadi suka kai hari makarantar yara a jihar Oyo tare da sace ɗalibai da wasu malamansu, lamarin da ya tayar ƙura da ke ci gaba da janyo wa gwamnatin Najeriya suka daga ƴan ƙasar.

  12. Gwamnatin Najeriya ta musanta batun ƙarin haraji kan sadarwa da mai

    Gwamnatin Najeriya ta ƙaryata rahotannin da ke cewa tana shirin ƙara sabbin haraji kan harkokin sadarwa ta waya da kuma man fetur, tana mai cewa waɗannan rahotanni ba su nuna gaskiyar manufofinta ba.

    Wannan bayanin ya biyo bayan wasu rahotanni da suka danganta da shawarwarin Asusun Lamuni na Duniya (IMF), wanda ya ce Najeriya na iya ƙara harajin VAT kan man fetur da hukumomin sadarwa ta waya domin ƙara kudaden shiga da tallafa wa ci gaba.

    Sai dai a wata sanarwa da ma’aikatar kudi ta fitar, ta bayyana cewa shawarar IMF ba dole ba ce, kuma ba ta zama doka ga Najeriya ba, domin duk wani mataki na haraji sai an bi tsarin doka da majalisa tare da la’akari da halin tattalin arzikin ƙasa.

    Gwamnatin ta ƙara da cewa har yanzu ana ci gaba da dakatar da harajin VAT kan man fetur, haka kuma an soke harajin sadarwar waya da aka gabatar kafin shekarar 2023, tana mai jaddada cewa babu wani sabon haraji da ake shirin ƙaƙabawa a yanzu.

  13. Jagororin jam'iyyun adawa na farin ciki kan hukuncin kotun ƙoli

    Jagororin jam’iyyun adawa na ci gaba da bayyana farin cikinsu kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke na dakatar da aiwatar da hukuncin da kotun tarayya ta yanke na soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa a ƙasar.

    Kotun ƙolin da ke zamanta a Abuja ta bayar da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da Alkali Peter Lifu ya yanke, wanda ya umarci hukumar zaɓe ta ƙasa INEC da ta soke rajistar jam’iyyun ADC da APP da AA da AP da ZLP.

    A hukuncin nata, kotun ta zargi alƙalin da saɓa wa umarnin da ta bayar tun farko, inda ta ce ya yi watsi da umarnin dakatar da sauraron shari’ar da kuma nuna halin girman kai a tsarin shari’a.

    Kotun ta bayyana matakin a matsayin mafi girman raini ga tsarin shari’a tana mai cewa alƙalin ya nuna halin rashin ladabi a aikin shari’a bisa ci gaba da shari’ar duk da umarnin da aka riga aka ba shi.

    A sakamakon haka, kotun ɗaukaka ƙolin ta amince da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin, tare da umartar cewa a dakatar da duk wani mataki na aiwatar da hukuncin har sai an kammala sauraron ƙarar gaba ɗaya.

    A baya dai, kotun babbar tarayya ta umarci INEC da ta soke rajistar jam’iyyun biyar, bisa zargin gazawarsu wajen cika sharuddan ƙundin tsarin mulki da ke ba su damar ci gaba da kasancewa a matsayin jam’iyyun siyasa a ƙasar.

  14. Kuɗaɗen kira da saƙonnin waya na iya ƙaruwa a Najeriya

    Kuɗaɗen kira da saƙonnin waya a Najeriya na iya ƙaruwa, bayan da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta fara duba farashin haɗin gwiwar kamfanonin sadarwa, karo na farko cikin shekaru takwas.

    Farashin da ake kira Mobile Termination Rate shi ne kuɗin da wani kamfanin sadarwa ke biyan wani idan abokin hulɗarsa ya yi kira zuwa wata hanyar sadarwa daban, kuma yana taka muhimmiyar rawa wajen tsara farashin kira da saƙonni.

    A halin yanzu, wannan farashi yana tsakanin naira 3.90 zuwa naira 4.70 a minti ɗaya, kuma masana na cewa duk wani ƙarin da aka yi zai iya jawo ƙarin kuɗi ga masu amfani.

    Sun kuma bayyana cewa sauye-sauyen tattalin arziki kamar faduwar darajar naira, hauhawar farashi da tsadar kayan aiki tun daga 2018 ne suka sa ake wannan bita, domin farashin ya dace da yanayin da ake ciki a yanzu.

  15. Tankokin Iran uku sun kaucewa shingen da sojojin ruwan Amurka suka yi

    Shafukan da ke sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa sun bayar da rahoton cewa tankokin mai uku na Iran sun kaucewa shingen ruwan da rundunar sojan ruwan Amurka ta kafa, karo na farko cikin watanni biyu.

    Binciken BBC Verify ya tabbatar da cewa tankokin, waɗanda ke ƙarƙashin takunkumi kuma mallakin Kamfanin Tankokin Mai na Iran, sun ketare layin shingen ɗauke da mai gabaɗaya, kafin su shiga Tekun Arabian Sea.

    Rahoton ya ƙara da cewa duk da cewa na’urorin da ke nuna matsayin tankokin suna aiki, ba sa bayyana inda suke nufa, abin da ke nuna yadda ake ci gaba da safarar mai duk da tsauraran takunkuman da ake fuskanta.

  16. 'Za a kafa wa Iran gidauniya ta dala biliyan 300 domin farfaɗo da tattalin arziƙinta

    Rahoton Reuters ya nuna cewa yarjejeniyar da ke tsakanin Amurka da Iran ta ƙunshi kafa wani wata gidauniyar zuba jari ta dala biliyan 300 ga Iran, inda sama da rabin kuɗin an riga an yi alƙawarin samar da shi daga kamfanoni masu zaman kansu.

    Majiyar da ta san batun ta ce an tsara gidauniyar ne domin samar da ƙarfafawar tattalin arziki ga ɓangarorin biyu domin kai wa ga yarjejeniya ta ƙarshe, kuma za a kira shi “gidauniyar gyarawa da cigaba”.

    Rahoton ya ƙara da cewa wannan gidauniyar ba na gwamnati ba ne, kuma ba ya ƙunshe da tallafin kuɗi daga gwamnatoci, sai dai kamfanoni daga Amurka, ƙasashen Gulf, Asiya, Afirka da Kudancin Amurka ne za su zuba jari.

    Zuba jarin da ake sa ran yi zai haɗa da fannoni kamar makamashi, sufuri, lodawa da sauke kaya da kuma masana’antu.

    Wata babbar majiya daga Iran ta ce Tehran ta fara neman dala biliyan 400 a matsayin diyya daga Amurka, amma Washington ta ƙi, wanda ya sa aka samar da wannan tsari na gidauniyar.

    Rahoton ya kuma nuna cewa wannan tsarin ya bambanta da tattaunawar da ake yi kan ɗage takunkumi da kuma sakin kadarorin Iran da aka daskare, kuma ba zai fara aiki ba sai an cimma cikakkiyar yarjejeniya mai gamsarwa.

    A cewar rahotanni, Iran za ta ci gajiyar wannan gidauniyar ne kawai idan ta cika wasu sharuɗɗa, ciki har da dakatar da shirinta na nukiliya.

  17. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.