Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Cristiano Ronaldo ya ci kwallo na 700 a tarihi
Cristiano Ronaldo ya ci kwallo na 700 ranar Litinin a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai a karawar da Portuagl ta je Ukraine.
Dan wasan mai shekara 34, shi ne ya ci wa Porugal kwallo a bugun fenariti a wasan da Ukraine ta yi nasara da ci 2-1.
Ya ci kwallo na 700 ne a tarihin sana'ar taka leda a wasa 973 da ya buga, hakan na nufin yakan zura kwallo a raga sau daya a fafatawa 458.
Kwallon da ya ci a Ukraine ya zama na 95 da ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Portugal, biye da dan kasar Iran, Ali Daei wanda ya ci wa kasarsa kwallo 109.
Ronaldo ya shiga jerin fitattun 'yan wasan da suka ci kwallo 700 ko fiye da haka.
Ronaldo tsohon dan wasan Manchester United da Real Madrid, yanzu yana taka leda a Juventus.