Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saura kwallaye 11 Ronaldo ya kafa sabon tarihi a duniya
Cristiano Ronaldo ya daga likkafar Portugal a gurbin gasar kwallon kafa ta nahiyar turai a shekarar 2020, inda ya ci mata kwallaye 98 bayan kwallaye ukun da ya zuba a ragar Lithuania.
Dan wasan mai shekara 34 na kulob din Juventus ka iya zama dan wasa na biyu da zai ci wa kasarsa kwallaye 100, idan ya zuba kwallaye biyu a ragar Luxemberg ranar Lahadi mai zuwa.
Ronaldo ya jefa kwallon farko a ragar ta hanyar fanareti, inda ya zura ta biyun bayan da ya tallafo kanta.
Pizzi da Goncalo Paciencia da kuma Bernado Silva na Manchester City sun zura nasu kawllayen kafin Ronaldo ya jefa ta uku.
Wannan ne dai karo na 9 da Ronaldo ke ci wa kasar tasa kwallaye uku a jere, inda bakwai daga ciki suka faru tun yana dan shekara 30.
Yanzu dai saura kwallaye 11 Ronaldo ya kamo dan wasan kasar Iran, Ali Daei wanda ya kafa tarihin cin kwallaye 109.