Wenger 'zai koma' AC Milan, ba za a tsawaita kwantaragin Sancho ba

Asalin hoton, Getty Images
Daraktan wasanni na Borussia Dortmundya yarda cewa ba zai bar dan wasan gaba na Ingila, Jadon Sancho, dan shekara 19, wanda ake rade-radin zai koma Manchester United ya tsawaita zaman sa a kulob din ba. (Kicker, via Mail)
Dan wasan gaba na Chelsea Tammy Abraham, mai shekara 21, na shirin juya wa Najeriya baya inda zai buga wa Ingila tamaula idan kocin kasar Gareth Southgate ya bukaci ya shiga tawagar da za ta fafata da Jamhuriyar Czech da Bulgaria a wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin turai ta shekarar 2020. (Telegraph)
Dan wasan baya na Tottenham Jan Vertonghen, mai shekara 32, wanda kwantaraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana, ya ce mai yiwuwa ya sanya hannu a sabon kwantaragi a kulob din. (London Evening Standard)
Tottenham sun soma tattaunawa da dan wasan kasar Belgium Vertonghen domin yiwuwar tsawaita kwantaraginsa. (Mail)
Da alama Los Angeles FC na son sayendan wasan gaba na Juventus Mario Mandzukic, dan shekara 33, wanda kulob din Manchester United ya dade yana zawarci.(Calciomercato - in Italian)
Rahotanni na cewa Manchester United na sansana dan wasan Tottenham dan kasar Belgium Toby Alderweireld, mai shekara 30, da zummar sayen sa idan aka bude kasuwar musayar 'yan wasa a watan Janairu. (Tuttosport, via Inside Futbol)
Tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger na cikin jerin sunayen koci-koci da ake sa ran za su maye gurbin kocin AC Milan Marco Giampaolo. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Arsenal na shirin kallon wasan da dan kasar Hungary Dominik Szoboszlai zai buga wa Red Bull Salzburg a karawar su da Liverpool a makon nan, a yayin da suke shirin sayen dan wasan dan shekara 18 a watan Janairu. (Football Insider)
Dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique zai tattauna da shugaban kulob din, Josep Maria Bartomeu, a yayin da ake ci gaba da zaman-tsama tsakanin 'yan wasa da hukumar gudanarwar kulob din. (ESPN)
Juventus da Inter Milan na shirin yin gumurzu a lokacin musayar 'yan wasa a watan Janairu a kan dan wasan Barcelona dan kasar Croatia Ivan Rakitic, mai shekara 31. (Calciomercato, via Caught Offside)
Kocin Porto Vitor Matos ya yi nisa wajen tattaunawa domin zama cikin jerin masu horaswa na kulob din Livepool da Jurgen Klopp ke jagoranta.(Liverpool Echo)
Dan wasan Manchester Uniteddan kasar Ivory Coast Eric Bailly zai ci gaba da jinyar raunin da ya ji a gwiwarsa har shekara mai zuwa. Dan wasan mai shekara 25 ya ji rauni ne lokacin wasan share-fage da suka fafata da Tottenham. (Sun)
Roma na sanya ido kan dan wasan Wolvesdan kasar Spain Adama Traore, mai shekara 23. (Calciomercato)
West Ham sun bai wa tsohon mai tsaron bayansu James Collins mukamin wakilin kulob din. (Football Insider)
Shugaban Tottenham Daniel Levy ne sanadin sanya hannu kan kwantaragin shekara hudu da dan kasar Faransa mai shekara 30 Moussa Sissoko ya yi. (Football Insider)
Matsin-lamba ne ya sa Arsenal suka tafi birnin Manchester ranar Litinin inda suka fafata da Manchester United da yammacin ranar saboda jam'iyyar Conservative ta sanya jami'anta a manya-manyan otal din da ke birnin sakamakon babban taron da take yi. (Sun)
Kocin Newcastle United Steve Bruce ba ya fuskantar matsin-lamba, duk da cewa kulob din shi ne na biyun karshe a tebirin gasar Firimiya bayan da suka sha kashi a hannun Leicester City da ci 5-0. (Times - subscription required)











