Real Madrid: 'Wajibi ne mu lashe komai da komai a Madrid'

Asalin hoton, Getty Images
Gabanin fafatawar Zakarun Turai da Real Madrid za ta yi da Club Brugge ranar Talata, hamshakin dan wasan gaban Madrid din Eden Hazard ya amsa wasu daga tambayoyin manema labarai game da halin da yake ciki a kungiyar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Game da wasansa na farko a Champions League:
"Ku duba yadda muke cin kwallaye da dama amma tun daga rashin nasarar da muka yi a Paris tilas ne mu ci dukkanin wasannin gaba.
"Da ma na yi tsammanin za a ci kwallaye masu yawa kuma wasan bai zo da sauki ba."
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Game da zuwansa Madrid:
"Na yi farin ciki sosai. Mutane suna tsammanin abubuwa da yawa daga gare ni kamar yadda ni ma nake kokarin yin hakan.
"Na sani zan sha suka amma dole na mayar da hankali domin lashe kyautuka. Tara muke ba mu cika goma ba, amma mu ne a saman teburin La Liga.
"Mun yi rashin nasara a Paris kuma ban fara wasanni ba saboda rauni amma yanzu garau nake ji na."
Game da zargin cewa ba ya tabuka komai, Hazard ya ce:
"Na san cewa magoya baya na so su ga manyan abubuwa daga gare ni kuma dole ne na ba su abin da suke so.
"Ai sun ga abin da na cimma a Faransa da Belgium da Chelsea. Zan kara kokari saboda su yi alfahari da ni."
Game da rashin kwarin gwiwa:
"Ba maganar kwarin gwiwa ba ce. Zidane ya fada min cewa na yi iya bakin kokarina. Wajibi ne na bai wa kungiyar kashi 100% domin babu maganar rauni kuma yanzu, na warke garau."
Game da lashe La Liga ko Champions League:
"Duka. Idan kana taka wa Madrid leda wajibi ne ka cinye komai da komai."












