Serie A: Balotell ya ci kwallo bayan kwana 1,468

Mario Balotelli

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Sai bayan kwana 1,468 sannan Balotelli ya ci kwallo a Serie A
An wallafa

Mario Balotell ya ci kwallo ta farko a Serie A bayan kwana 1,468 amma duk da haka Napoli ta yi nasara a wasan kan Brescia a filin wasa na San Paolo.

Dries Mertens na Napoli ne ya bude filin da kwallonsa ta hudu da ya ci a kakar bana kafin daga bisani Kostas Manolas ya kara ta biyu ana dab da tafiya hutun rabin loakci.

Brescia sun yi kaimi bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, sai dai na'urar VAR ta hana kwallon da Sandro Tonali ya ci inda ta ce an yi laifi kafin ta shiga raga.

Balotelli ya ci kwallon tasa da ka domin dawo da Brescia cikin wasan amma Napoli ba ta bari an farke ta biyun ba.

Rabon da dan kasar Italiyan ya ci kwallo a Serie A tun 22 ga watan Satumban 2015 a wasan da AC Milan ta ci Udinese 3-2, kafin ya koma Nice da kuma Marselle a kasar Faransa.

Dan wasan mai shekara 29 ya koma kasar Italiya a watan Agusta domin buga wa Brescia wasa a garin da aka haife shi a yarjejeniyar shekara uku.

Sakamakon ya bai wa Napoli damar daidaita zamanta a mataki na hudu a teburin Seria A, ita kuma Brescia tana ta 14.