Man United: Pogba zai dawo taka-leda a gasar Carabao

Paul Pogba

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rabon Pogba da wasa tun wanda suka yi 1-1 da Southampton a watan Agusta
An wallafa

Dan wasan tsakiyar Man United Paul Pogba zai dawo taka-leda a wasan da United za ta kara da Rochdale a gasar Carabao Cup ranar Laraba.

Raunin da dan wasan mai shekara 26 ya ji a idon-sawunsa ya hana shi buga karawar da kasarsa Faransa ta yi da Albania da kuma Andorra na neman cancantar shiga Kofin Duniya a watan nan.

Sannan kuma bai buga wasa uku ba tare da Man United - biyu a Premier daya a gasar Europa.

"Babu mamaki ya buga wasu 'yan mintuna a wasan Rochdale," koci Ole Gunnar Solskjaer ya fada.

Bayan karawa da Rochdale masu buga gasar League One, United za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan Premier mako na 7 ranar Litinin a Old Trafford.