West Ham vs Man United: United ta sha kashi

Asalin hoton, Getty Images
Kwallaye daga Andriy Yarmolenko da kuma Aaron Cresswell ne suka bai wa West Ham nasara kan Man United, wadanda rabon da su ci wasan waje a Premier tun Fabarairu.
Yarmolenko ne ya bude ragar United din ana gab da tafiya hutun rabin lokaci, inda ya dada wa De Gea kwallon bayan abokan wasansa Mark Noble da Felipe Anderson sun shirya ta har zuwa cikin yadi na 18.
Cresswell shi kuma ya kammala nasarar ga West ham bayan an dawo daga hutun daga wani kayataccen bugun tazara da ya buga zuwa makogaron ragar De Gea daga bangaren dama.
Ya kamata Juan Mata ya farke kwallon farko minti biyu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci amma sai ya kasa cilla kwallon inda ya dace bayan fasin din da Andreas Pereira ya yi masa a kusa da turken bangaren hagu.
Rashford bai iya ci gaba da wasa ba kuma Jesse Lingard ya karbe shi a minti na 61 bayan ya fadi kasa, abin da ke nuna alamun yanzu haka ya ji rauni.
Fitar tasa ta kara wa Hammers kwarin gwiwa ganin cewa yana cikin zaratan 'yan wasan gaban da ke kai kora zuwa bayan West Ham din.
Wanda ya karbe shi, Jesse Lingard, sau bakwai kacal ya taba kwallon a minti 29 da ya buga na wasan tare da yin shot daya da kuma fasin shida.
Sakamakon ya daga West Ham zuwa mataki na 4, inda ta bar United a mataki 7 da maki uku tsakaninta da 'yan hudun farko.
Sakamakon wasannin Lahadi:

Sakamakon wasannin Asabar:












