Fifa FIFPro 11: Ba a furta sunan Ronaldo ba a cikin tawagar

Tawagar maza ta Fifa FIFPro 11

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Fifa ba ta furta sunan Ronaldo ba lokacin da take bayyana sunayen 'yan tawagar maza ta Fifa FIFPro 11
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Idan ana maganar Ronaldo abin da zai fara zuwa zukatan masoya kwallon kafa shi ne kyautar gwarzon dan kallon duniya saboda an shekara sama da 10 ana ganinsa a dararen karbar kyautuka daban-daban.

Sai dai ba a gan shi ba a daren jiya Litinin a birnin Milan na Italiya yayin da Fifa ta bayyana sunan Lionel Messi a matsayin gwarzon dan kwallon duniya karo na shida.

Wani abu da ba kasafai aka saba gani ba shi ne, lokacin da mai jagorantar shirin yake bayyana sunayen 'yan tawagar kwararru maza ta Fifa FIFPro 11 bai fadi sunan Cristiano Ronaldo ba duk da cewa yana cikin tawagar.

Sunayen mutum 10 aka furta. 'Yan wasa 10 - dukkaninsu tsaye a kan dandamali - sun jeru reras. Kai tsaye kuma aka fara raba masu kyautukansu.

Ba a fadi sunan Ronaldo ba amma kuma shafin Fifa na intanet ya tabbatar da sunansa a cikin 'yan tawagar.

To me ya hana shahararren dan kwallon halartar taron? Juventus za ta ziyarci Brescia ranar Talata sa'a 24 bayan bikin - wasan da koci Maurizio Sarri ya ce babu tabbas ko Ronaldo zai buga saboda gajiya.

Amma abokin wasansa De Ligt ya samu halarta - nisa tsakanin Turin da Milan rabin tafiyar zuwa Brescia ne - yada zango kawai za a yi.

Tasawirar Turin zuwa Brescia

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto, Birnin Milan yana tsakiyar Turin ne (inda Juventus take) da Brescia, inda Juventus za ta ziyarta a wasan Serie A ranar Talata da karfe 8:00 agogon Najeriya

Shi ma Messi zai fafata a ranar Talata a wasa mai zafi tsakanin Barcelona da Villareal. Tafiyar minti 90 da zai yi a jirgi daga Milan zuwa gida Barcelona ta fi wadda Ronaldo zai yi a mota zuwa Turin nisa.

Ko ma dai mene ne dalilin rashin zuwansa, Ronaldo yana cikin farin ciki a daren Litinin din, inda ya wallafa wannan hoton ana dab da kammala taron.

Kauce wa Instagram
Ya kamata a bar bayanan Instagram?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a Instagram

"Hakuri da juriya abubuwa ne guda biyu da suke bambance kwararre daga dan koyo," ya rubuta a Instagram.

"Duk abin da ya kai kololuwa a yau to a matsayin karami ya fara. Ba za ka iya yin komai da komai ba, amma ka yi iya bakin kokarinka domin cimma burinka. Ka sani komai nisan dare gari zai waye."