Bayern Munich: 'Yan wasanta za su kaurace wa tawagar Jamus

An wallafa

Shugaban kungiyar Bayern Munich Uli Hoeness ya yi barazanar hana 'yan wasan Bayern din buga wa tawagar kasar Jamus wasa idan har aka sauya mai tsaron ragarsa Manuel Neuer a matsayin lamba 1 na tawagar.

Shugaban ya yi wannan barazana ce yayin da Jamus ke yunkurin maye gurbin Manuel Neuer da Ter Stegen na Barcelona a matsayin golan tawagar lamba 1.

Ter Stegen dai ya nuna kansa a 'yan kwanakin nan a Baarcelona, inda har ma ya shiga cikin 'yan ukun karshe da Fifa ta zaba a matsayin gwarazan gololi na 2019.

Golan mai shekara 27 ya kalli wasannin da Jamus ta yi rashin nasara a hannun Netherlands da ci 2-4 da wanda ta doke Northen Ireland da ci 2-0 daga benci a wasannin cancantar shiga Kofin Duniya.

Haka ya koma sansanin atsaye na Camp Nou ransa a bace ba tare da ya tsare wa kasarsa raga ba.