Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fifa The Best: Messi ya doke Ronaldo da Van Dijk
Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta karrama gwarazan 'yan wasa na shekarar 2019, inda Messi ya lashe kyautar ta Fifa The Best karon farko tun bayan kaddamar da ita a 2017.
Wannan ne karo na shida da ake zabar Messi a matsayin gwarzon dan kwallon duniya - 2009 da 2010 da 2011 da 2012 da 2015.
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ne ya lasahe kyautar koci mafi hazaka yayin bikin da ya gudana a birnin Milan na Italiya.
Klopp ya doke abokan hamayya da suka hada da Pep Guardiola da kuma Mauricio Pochettino, wadanda dukkansu ke jagoranci a gasar Premier.
Sai kuma Megan Rapinoe 'yar wasan tawagar kasar Amurka wadda ta lashe kyautar a matsayin gwarzuwar kwallon mata.
Alisson Becker mai tsaron ragar Liverpool shi ne golan da ya fi saura hazaka kuma shi a aka bai wa kyautar, inda ya doke Ter Stegen na Barcelona da kuma Ederson na Manchester City.
A bangaren masu horarwa a kwallon mata kuma Jill Ellis ce ta lashe kyautar bayan ta jagoranci tawagar kasar Amurka, inda suka lashe Kofin Duniya na 2019 a kasar Faransa.
Dan shekara 18 Daniel Zsori, shi ne ya lashe kyautar Puskas ta kwallon da aka ci mafi kayatarwa.
Ya ci kwallon a minti na 93 bayan ya yi tsallen badake ya watse a wasan da kungiyarsa ta Debrecen ta yi da Ferencvaros a gasar lig ta kasar Hungry.
'Yan wasan tawagar FIFPro
An kuma zabi kwararrun 'yan wasan da suka hada mutum 11 na tawagar Fifa, wadanda ake kira FIFPPro 11. Su ne:
'Yan wasan baya - Matthijs de Ligt (Ajax and Juventus/Netherlands), Sergio Ramos (Real Madrid/Spain), Virgil van Dijk (Liverpool/Netherlands), Marcelo (Real Madrid/Brazil).
'Yan wasan tsakiya - Luka Modric (Real Madrid/Croatia), Frenkie de Jong (Ajax and Barcelona/Netherlands), Eden Hazard (Chelsea and Real Madrid/Belgium)
'Yan wasan gaba - Kylian Mbappe (Paris St-Germain/France), Cristiano Ronaldo (Juventus/Portugal), Lionel Messi (Barcelona/Argentina)