Barcelona vs Villareal: Barca ta ci wasa amma Messi ya ji rauni

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Barcelona ta samu nasara kan Villareal da kyar a wasan Laliga mako na shida amma Messi ya samu rauni a wasan farko da aka fara da shi a La Ligar bana.

Dukkanin bangarorin biyu ba su yi wani kokari ba a falle na biyu na wasan, kuma Villareal za su yi danasanin cewa sun kara matsa wa bayan Barcelona kafin wasa ya tashi da su 2-1.

Griezman ne ya fara cin kwallo a minti na shida kafin Arthur ya kara ta biyu minti tara bayan haka.

Santi Cazorla ne ya tabbata ya farke wa bakin kwallo daya ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, sai dai ba ta isa ta hana a doke su ba a filin wasa na wasa na Camp Nou.

Barcelona dai ta farfado ne daga rashin nasara a hannun Granada da ta yi, sai dai raunin da Messi ya ji ka iya bata murnar da 'yan Barca suke yi.

Ya samu ya karasa minti 45 na farko amma Valverde bai yadda da kasassaba ba, inda ya sauya shi da Dembele kuma ba a dawo filin wasan da shi ba.

Sai nan gaba ne za a san irin raunin da ya ji kwana daya bayan Fifa ta bayyana shi a matsayin gwarzon dan wasan duniya na 2019.