Milan Derby: AC Milan ta sha kashi har gida

Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan ta lakada wa abokiyar hamayyarta AC Milan duka har gida da ci 2-0, godiya ga Marcelo Brozovic da Romelu Lukaku da suka jefa kwallayen.
Wasan hamayya ne na birnin Milan, wanda babu kamarsa a gasar Serie A ta Italiya, kuma da wannan nasara Inter ta bai wa Juventus tazarar maki biyu a saman teburi.
Marcelo Brozovic ne ya fara jefa kwallon farko a minti na 49, kafin daga bisani Lukaku ya kara ta biyun bayan Nicolo Barella ya taso masa kwallon a sama, inda shi kuma ya jefa ta raga da kansa kamar dai yadda ya saba, a minti na 78.
Wannan ita ce kwallo ta uku da dan kasar Belgium din ya zura a raga a Serie A ta bana, yayin da yake fuskantar kalaman wariya daga wasu masoya kwallon kafa a Italiya.
Nasarar ta zo ne bayan canjaras da Inter ta yi da Slavia Prague a wasan Zakarun Turai na Champions League a daren Talata.
Ganin cewa kungiyoyin biyu suna amfani ne da filin wasa na Stadio Gluseppe Meazza a matsayin gidansu, ma iya cewa darace ta ci gida kawai.







