Chelsea vs Liverpool: Chelsea ta yi rashin nasara har gida

Asalin hoton, @LFC
Liverpool ta ci gaba da jan zarenta a wasa tsakaninta da Chelsea da ma Premier baki daya, inda Alexander-Arnold da Roberto Firmino suka hidimta mata a filin wasa na Stamford Bridge.
Kwallon da Ngolo Kante ya sharara a ragar Liverpool din a minti na 71 ta yi wa Chelsea kaimi kuma ta so ta farke ta biyun ma a hare-haren da Mason Mount da Batsuayi suka kai a cikin minti goman karshe na wasan.
Chelsea har yanzu ba ta ci wasa a gida ba a kakar bana, yayin da har yanzu ba a doke Liverpool ba a wasa shida na Premier,
Alexander-Arnold ne ya fara jefa kwallo a ragar Chelsea a minti na 14, kafin daga bisani Roberto Firmino ya kara ta biyu a minti na 30.
Game da wasan
Wasa daya kacal Chelsea ta ci a haduwa 10 ta baya-bayan nan da suka yi a Premier - canjaras 5, rashin nasara 4.
Ita kuwa Liverpool ta ci wasa shida daga cikin karawa 11 ta karshe da suka yi a Stamford Bridge a Premier.
Chelsea ta jefa kwallo a dukkanin wasa 20 na baya-bayan nan tsakaninta da Liverpool da suka yi a kowacce gasa.
Sakamakon wasannin Lahadi:

Sakamakon wasannin Asabar:








