Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yan matan Najeriya sun lashe kofin Afirka
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1
Tawagar mata ta Najeriya ta sake lashe kofin mata na Afirka na gasar kwallon kwando ta AfroBasket a Senegal.
D'Tigress sun doke mai masaukin baki Senegal da maki biyar a wasan karshe.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake wallafa sakon Twitter na hukumar kula da kwallon kwando ta duniya, yana cewa duka al'ummar kasar na murnar nasarar da 'yan matan suka samu:
D'Tigress sun wallafa a shafinsu na Twitter cewa an kai ruwa-rana a gasar - sannan suka mika godiya ta musamman ga dukkan magoya bayansu: