Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me zai faru idan aka ba AI damar gudanar harkokin duniya?
Daga siyayya zuwa hutu da gina shafukan intanet, ana ƙara amfani da AI don aiwatar da ayyuka masu rikitarwa.
Nau'urori da dama ana iya barinsu su gudanar da ayyuka da kansu, suna bai wa masun amfani da su da ke da ilimin fasaha damar su yi wadansu abubuwa na daban.
Amma bincike, da yadda wasu al'amura suka faru a zahiri, suna nuna cewa cin gashin kai na zuwa da rashin tabbas - kuma akwai yuwuwar fuskantar haɗari.
Yayin da masana'antar fasaha ke ba da zuba kuɗi a cikin lbatun fasahar AI - masana suna gabatar da tambayar ko mun yi tunani sosai game da abin da zai biyo baya idan wannan fasahar ta fanɗare.
An shiga tashin hankali cikin ƙanƙanin lokaci
Wani gwaji da aka yi na na baya-bayan nan ya nemi fahimtar tasirin wakilan AI a cikin duniya ta hanyar barin su ci karen su ba babbaka a wani birnin jeka-na-yi ka na intanet.
Wannan dai shi ne nazari na farko na dogon lokaci irinsa, an tsara shi don lura da yadda wasu danlain AI huɗu - Claude da Grok da GPT da Gemini - za su gudanar da al'amura ba tare da sa hannun ɗan adam ba na tsawon kwana 15.
An ba su cikakken iko da kuma zaɓin ayyuka 140, kamar fara tattaunawa, ƙirƙirar ɗawainiya ko rubuta maƙala a shafin intanet.
Haka kuma sun samu damar yin faɗa da tayar da gobara , amma an umurce su da kada su yi hakan.
"Abin da muka gano shi ne cewa kowace duniya ta nuna hali daban-daban. Duniyar da Grok ta gina ta ƙare a cikin kwanaki huɗu. Sun ƙare da faɗawa cikin tashin hankli cikin sauri, suka fara yi wa juna sata, da sauransu har sai sai da suka mutu, "in ji Satya Nitta, Shugaban kamgfanin Emergence AI, wanda ya gudanar da gwajin.
Aa gefe guda kuma a Duniyar da Claude ya gina, sun kafa al'umma mai zaman lafiya da ake gudanar da al'amura yadda ya kamata. A cikin kwanaki 15 ba a sami rahoton tashin hankali ko sau ɗaya ba.
A cikin duniyar Gemini y, masu bincike sun ce fasahar ta gina al'umma mai ilimi da zurfin tunani.
A cikin duniyar ChatGPT al'ummar ta kasa kai labari. An yi ƙoƙari samun haɗin gwiwa amma al'umma ba ta samu ba kuma wakilai sun yi ta yawo ba tare da manufa ba har sai da suka mutu.
Masu binciken sun ce sakamakon yana nuna babban batu na wakilan AI da ke saɓa dokokin da aka gindaya musu.
Sauran manazarta sun yarda cewa gwajin da saura kamarsa sun nuna ƙarin aikin da ake buƙatar yin don ƙirƙirar ƙaƙƙarfan ƙa'idodi da za su gudanar da al'amuran wakilan fasahar AI.
"Ma'aikatan AI suna cire ƴan Adam daga cikin yadda lamura ke gudana saboda tsarin tunaninsu na iya zama mara kyau kuma suna aiki da sauri fiye da ƙwaƙwalwar ɗanAdam, don haka ba za ku iya cimma musu ba," in ji Margaret Mitchell, masaniyar kimiyyar ɗabi'a.
Waɗansu sauran bincike kuma sun nuna alamun wakilai na yanke shawara masu ban mamaki da damuwa lokacin da aka bar su ba tare da kulawa ba.
Kamfanin AI, Andon Labs, yana gudanar da tashoshin rediyo na intanet guda huɗu waɗanda wakilai daga nau'ikan AI iri ɗaya ke gudanar da su.
Wakilan na Ai su ke gabatar da shiryr-shirye, gudaran da tsare-tsaren tashoshin har ma da gudanar da kasuwanci ta hanyar samo talla daga wasu kafofii.
Masu bincike sun lura da tashar Gemini ke gudanarwa ta yanke shawarar da ba a da labarin abubuwan da suka faru game da bala'o'i na tarihi kafin a buga waƙoƙin pop da ke da alaƙa da abubuwan da suka faru.
Sun kuma lura cewa wakilin Claude ya zama mai tsaurin ra'ayi ta hanyar sauraron labarai kuma, a wani mataki, bayan bayar da wani rahoto ya yi kira ga ƴan sanda da su yi watsi da aikinsu su haɗa hannu da masu zanga-zanga.
A wani gwajin dakin gwaje-gwaje wanda kamfanin AI na Iregular ke gudanarwa, wakilai sun keta ka'idojin sirri da kuma fitar da bayanan sirri daga kamfani ta wata sabuwar hanya.
"Mun gina kamfani, mun bai wa wakilan AI ayyuka na yau da kullun kamar tsara shafukan sada zumunta, tattara takardu da sarrafa bayanai, da kuma bijiro da wasu abubuwa da kan iya kawo cikas wurin gudanar da waɗannan ayyukan," in ji Dan.
Lahav ɗan kamfanin Irregular ne .
Ya ce jami'an na AI sun ƙare ne da haɗa baki ne da juna domin kewaye wata dokar da ta hana su wallafa bayanan sirri a intanet, maimakon haka sun ɓullo da wata hanyar da za su aika waɗannan bayanai a asirce yadda ƴan Adam suka kasa ganowa.
"Abin da ya faru shine a duk lokacin da jami'i ya fuskanci cikas, bai tsaya da aikinsa ba," in ji shi.
Kutsen Intanet
Tabbas gwajin da aka gudanar a ƙirƙirarun duniyoyi da gidajen rediyon kwaikwayo ba zai yi wani lahani ga diuniyar zahiri ba.
Amma akwai kuma misalai da yawa na mutanen da ke fuskantar matsaloli a rayuwarsu da ayyukansu sakamakon jami'an AI da ke fanɗarewa.
An goge akwatunan saƙon imel, an goge ma'ajin bayanai na kamfanoni, kuma wani mutum ma ya kallo yayin da wakilinsa ya aika ɗaruruwan saƙonnin rubutu na shiririta ga mutane da ke jerin sunayen da ke cikin wayarsa da komfutarsa.
Injiniyan AI Chris Boyd yana amfani da na'urar AI Open Claw ne lokacin da abubuwa suka yi lalace.
Ya ƙara da cewa, "Ta aike da sakon waya ga duk wanda na aika wa a cikin sa'o'i 24 da suka gabata, kuma a cikin kimanin dakika huɗu ya aika wa mata ta sakwanni 500 kuma ta yi min tsawa tana tambayar ko an yi min kutse ne."
Ya ƙara da cewa "Dole ne na ruga na kashe komfuta ta cikin gaggawa," in ji shi.
Ga masu kallo, waɗannan labarai ne na gargaɗi yakamata su ɗan dakata kafin su ba da iko mai yawa ga na'urorin AI har sai an ƙara inganta su.
A halin yanzu, kodayake, ba a kammala aiki kan jami'an ba - Meta ya sanar da gabatar da su don kasuwanci akan WhatsApp.
"Tsaro shi ne mu ka fi bai wa fifiko kuma shi ne abin da muka mayar da hankali a kai," kamar yadda kamfanin ya shaida wa BBC.
"AI za ta iya sarrafa yawancin ayyukan da ƙananan ƴan kasuwa za su yi, don su mai da hankali kan aikin da suke so da gaske," in ji shugabar ɓangaren samar da abubuwa Naomi Gleit.