Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gasar kofin duniya 2026: Netherlands da Japan sun raba maki a tsakaninsu

Takaitaccen Bayanin Wasa

Netherlands 2 , Japan 2 at Full time
Netherlands
Japan
Full time
Hutun rabin lokaci Netherlands 0 , Japan 0

Key Events

Netherlands

  • V. van Dijk Goal 51 minutes
  • C. Summerville Goal 64 minutes

Japan

  • K. Nakamura Goal 57 minutes
  • D. Kamada Goal 89 minutes
Ba da ƙwallo a ci
Netherlands,R. Gravenberch (51 minutes, 64 minutes)
Japan,T. Kubo (57 minutes), K. Ogawa (89 minutes)

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu tare da taimakon AI

  1. Nan muka kawo karshen shirin

    Da fatan za ku ci gaba da bibiyar yadda muke kawo muku wasannin gasar cin kofin duniya kai tsaye a kowace rana.

    Sunana Mohammed Abdu Mamman Skeeper Tudun wada Kano ke muku fatan asuba ta gari.

  2. Wasannin da za a buga ranar Litinin

  3. Yadda aka murza leda a karawar

  4. An tashi wasan, Netherlands 2-2 Japan

    An tashi wasan rukuni na shida da cin kwallo 2-2 tsakanin Netherlands da Japan.

  5. , Netherlands 2-2 Japan

    An yi karin minti shida.

    Abin mamaki sai a zagaye na biyu ne aka ci kwallo huɗu, biyu daga Netherlands da biyu daga Japan.

  6. GOAL - Netherlands 2-2 Japan, Daichi Kamada

    Magoya bayan Japan sun barke da sowa.

    Bugun kusurwa daga Koki Ogawa, inda mai tsaron raga ya sa hannu, duk da haka ta fada raga, wanda ya taba kwallon na karshe shi ne Daichi Kamada.

  7. Canjin ɗan wasa, Netherlands 2-1 Japan

    Cody Gakpo ya fita, inda Bryan Brobbey na Sunderland ya maye gurbinsa.

  8. Katin gargaɗi ga Depay, Netherlands 2-1 Japan

    Depay wanda bai dade da shiga wasanba, ya karbi katin gargadi, sakamakon ketar da ya yi wa Shogo Taniguchi.

  9. , Netherlands 2-1 Japan

    Kasa da minti 10 ya rage, ko Japan za ta farke kwallon ko kuwa?

  10. Japan ma ta yi canjin ƴan wasa uku rigis, Netherlands 2-1 Japan

    Waɗanda aka canja: Takefusa Kubo da Tsuyoshi Watanabe da kuma Ritsu Doan.

    Waɗanda suka shiga fili: Koki Ogawa da Takehiro Tomiyasu da kuma Yukinari Sugawara.

  11. Netherlands ta canja ƴan wasa uku rigis, Netherlands 2-1 Japan

    Tawagar Netherlands ta yi canjin yan wasa uku, domin ta kara karfi a wannan zagaye na biyun.

    Memphis Depay ya canji Donyell Malen, Crysencio Summerville ya fita, kuma Teun Koopmeiners ya maye gurbinsa da kuma Quinten Timber da ya canji Tijjani Reijnders.

  12. , Netherlands 2-1 Japan

    Kubo daga Japan ya samu dama ya buga daf da kusan gidan Neterlands, amma kwallon ta yi sama sosai, sai dai ta yi kyau.

  13. GOAL - Netherlands 2-1 Japan, Crysencio Summerville

    Kwallo ce mai kyau Summerville ya samu daf da gidan Japan, haka ya sa kafar hagu ya buga ta kuma faɗa raga.

    Kamar ba shi aka bai wa katin gargadi ba, sakamakon ketar da ya yi.

  14. An bayar da katin gargadi, Netherlands 1-1 Japan

    An bai wa Summerville katin gargadi sakamkon ketar da ya yi.

  15. GOAL - Netherlands 1-1 Japan, Keito Nakamura

    Jaapn ta farke ta hannun Nakamura, karawar ta koma 1-1.

    Tun da suka koma zagaye na biyu Japan ta zauna a gida, amma da aka fara zura mata kwallo, hakan ya sa ta fito ta farko.

    Da kyar ne idan za a ci kwallaye da yawa a wasan nan.

  16. , Netherlands 1-0 Japan

    Virgil van Dijk ya ci wa Liverpool kwallo takwas a kakar da ta wuce, yanzu kuma ya ci Japan a gasar cin kofin duniya.

  17. GOAL - Netherlands 1-0 Japan, Virgil van Dijk

    Minti shida da shiga zagaye na biyu ɗan wasan Liverpool, Virgil van Dijk ya ci ƙwallo da kai.

  18. , Netherlands 0-0 Japan

    Netherlands tana yin kokari tun da suka koma zagaye na biyu a karawar nan.

  19. , Netherlands 0-0 Japan

    Virgil van Dijk ya raba kwallo sau 68 a zagayen farko - shi ne mafi kwazo daga ɗan wasan Netherlands tun daga 1966 a gasar cin kofin duniya.

  20. , Netherlands 0-0 Japan

    An kuma zagaye na biyu, za kuma a kammala minti 45.

    Wannan karon Japan ce ta take kwallon.