Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Lahadi, 14 ga watan Yuni, 2026.

Rahoto kai-tsaye

Aisha Babangida da Isiyaku Muhammed

  1. Ƴanbindiga sun yi garkuwa da jami'in ma'aikatar tsaron Haiti

    Rahotanni daga ƙasar Haiti na cewa wasu mutane masu ɗauke da makamai sun yi garkuwa da babban jami'in ma'aikatar ministan tsaron ƙasar a babban birnin ƙasar, Port-au-Prince.

    James Boyard, wanda fitaccen masanin harkokin tsaro ne, kuma babban sifeton 'yan sanda na ƙasar, ana kyautata zaton shi ne jami'i mafi girma da aka yi garkuwa da shi a Haiti cikin 'yan shekarun nan.

    Wasu mutane biyu da suka san yadda lamarin ya faru sun tabbatar wa jaridar The New York Times da batun sace shi. Kafofin watsa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa an yi garkuwa da Boyard ne a yankin Bourdon, ɗaya daga cikin wuraren da ake ganin har yanzu suna da ɗan tsaro a babban birnin kasar.

    Ƙasar Haiti, wadda ita ce ƙasa mafi yawan al'umma a yankin Karebiyan, ta shafe shekaru tana fama da tashe-tashen hankula da ayyukan ƙungiyoyin masu laifi. Rikicin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da raba sama da mutum miliyan ɗaya da muhallansu.

  2. Ana kaɗa ƙuri'ar ƙayyade yawan al'ummar Switzerland

    Masu kaɗa ƙuri'a a ƙasar Switzerland na yanke hukunci a yau kan wata shawara da ke neman kayyade yawan al'ummar ƙasar zuwa miliyan goma.

    Fiye da kashi ɗaya cikin huɗu na mutanen ƙasar miliyan 9.1 ba 'yan ƙasa ba ne, kuma wannan shiri ya fito ne daga jam'iyyar masu ra'ayin riƙau ta Swiss People's Party.

    Jam'iyyar ta ce idan masu kaɗa ƙuri'a suka amince da shawarar, hakan zai rage matsin lamba kan gidaje, da ayyukan gwamnati da kuma muhalli.

    Sai dai gwamnati da shugabannin harkokin kasuwanci da kuma sauran manyan jam'iyyun siyasar ƙasar na adawa da wannan mataki, suna masu cewa hakan zai hana Switzerland samun ma'aikatan da take matuƙar buƙata, tare da kawo cikas ga yarjejeniyoyin da aka daɗe ana kullawa da tarayyar Turai.

    Babu wata ƙasa da ta taɓa yunƙurin sanya iyaka kai tsaye ga yawan al'ummarta a baya, kuma ana sa ran duniya za ta zura ido sosai kan sakamakon ƙuri'ar da za a yi a Switzerland.

  3. China ta nuna fushinta bayan Amurka ta zargi wasu kamfanonin ƙasar ''da tallafa wa soji''

    Mahukuntan a China sun nuna fushinsu, bayan wata sanarwar da Washington ta fitar a farkon makon nan cewa ta ƙara wasu kamfanonin kasar cikin jerin kamfanonin da Ma'aikatar Tsaron Amurka (Pentagon) ke zargi da tallafa wa rundunar sojin China.

    Ma'aikatar Kasuwancin kasar ta ce a ranar Asabar ba ta gamsu ko kaɗan da wannan mataki ba, wanda ya sa aka saka kamfanoni irin su kamfanin kera motoci na BYD da kuma katafaren kamfanin kasuwancin intanet na Alibaba cikin wannan jeri.

    Ma'aikatar ta kuma yi gargaɗin cewa idan har Amurka ba ta yi mi'ara koma baya ba, Beijing za ta ɗauki matakan ramuwar gayya.

  4. Manyan hafsoshin sojin Najeriya da matsalar tsaro ta rutsa da su

    A Najeriya, sacewa da mutuwar tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar, Manjo Janar Abubakar Rabe su haifar da muhawara, musamman a kafofin sadarwa, inda wasu ke fargabar lamarin na ta'azzara.

    A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ne gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa tsohon hafsan tsaron ya rasu bayan kwanaki a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi.

    Yadda ƴanbindiga suka riƙa fitar da bidiyon janar ɗin tare da matarsa ya ja hankali matuƙa, inda ake ganin matsayinsa ya wuce haka, har wasu ke cewa alamu na nuna cewa kowa zai iya shiga matsalar.

  5. Yau za mu saka hannu a yarjejeniya da Iran - Amurka

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa za a rattaba hannu kan yarjejeniya da Iran wadda za ta hana ƙasar samar da makamin nukiliya, tare da tabbatar da sake buɗe mashigar Hormuz a yau Lahadi.

    Sai dai wannan saƙo da shugaban ya wallafa a shafinsa na sada zumunta ya zo ne bayan kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya nuna har yanzu babu lokacin sanya hannu kan yarjejeniyar.

    Wakilin BBC ya ce Iran ta fi nuna taka-tsantsan kan lokacin sanya hannun, watakila saboda har yanzu ba su daddale komai game da batun ba.

    Jiya Asabar ita ma Pakistan, wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen sasanta ɓangarorin, ta ce ana sa ran kammala yarjejeniyar cikin sa'o'i 24 masu zuwa, tare da bayyana cewa ana shirye-shiryen sanya hannu ta Internet.

  6. Buɗewa

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Asabar.

    Aisha Babangida ce ke fatan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.