Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan hafsoshin sojin Najeriya da matsalar tsaro ta rutsa da su
A Najeriya, sacewa da mutuwar tsohon mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar, Manjo Janar Abubakar Rabe su haifar da muhawara, musamman a kafofin sadarwa, inda wasu ke fargabar lamarin na ta'azzara.
A ranar Asabar, 13 ga Yunin shekarar 2026 ne gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa tsohon hafsan tsaron ya rasu bayan kwanaki a hannun waɗanda suka yi garkuwa da shi.
Yadda ƴanbindiga suka riƙa fitar da bidiyon janar ɗin tare da matarsa ya ja hankali matuƙa, inda ake ganin matsayinsa ya wuce haka, har wasu ke cewa alamu na nuna cewa kowa zai iya shiga matsalar.
Sai dai gwamnatin Katsina ta bayyana a wata sanarwa da kwamishinan tsaron cikin gida, Nasiru Mu'azu ya fitar cewa tsohon hafsan ya rasu ne sakamakon ta'azzarar ciwon siga da hawan jini da yake fama da su yayin da yake tsare a hannun masu garkuwar.
Sai dai ba wannan ba ne karon farko da matsalar da ta rutsa da manyan hafsoshin Najeriya, inda wasu suka rasu, wasu kuma suka tsira bayan ko dai biyan kuɗin fansa ko ɗauki ba daɗi.
Bayan hafsoshin kuma, akwai ɗaruruwan ƙananan sojojin da matsalolin tsaron ya rutsa su.
Sai dai wasu ba ƴanbindiga ba ne ko Boko Haram suka kashe su, akwai irin su Janar Alƙali da rikici ne ya rutsa da su.
Wannan ya sa BBC ta rairayo wasu manyan hafsoshin tsaron ƙasar da suka fada cikin ƙomar matsalolin tsaro tare da kalato rahoton jaridar ICIR.
Manjo Janar Idris Alkali
A watan Satumba na shekarar 2018 ne wasu mutane suka tare Manjo Janar Idris Alƙali mai ritaya a jihar Filato a hanyarsa ta zuwa gona, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwarsa.
Lamarin ya auku ne a garin Dura-Du da ke ƙaramar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.
Janar Alƙali ya taɓa riƙe muƙaman babban daraktan gudanarwa a hedikwatar sojin ƙasan Najeriya.
Bayan makonni na bincike da sojoji suka gudanar aka gano gawarsa a cikin wani kududdufi a ƙauyen Guchwet da ke yankin Shen a Jos ta Kudu.
Air Chief Marshal Alex Badeh
A ranar 19 ga Disamba, 2018, tsohon babban hafsan tsaron Najeriya tsakanin 2014 zuwa 105 Air Chief Marshal Alex Badeh ya gamu da ajalinsa a kan hanyar komawa gida daga gonarsa.
Lamarin ya auku ne bayan ƴanbindinga sun buɗe masa wuta a cikin motarsa a hanyar Abuja zuwa Keffi da ke jihar Nasarawa.
A lokacin harin, lamarin ya ɗauki hankali matuƙa, musamman ganin inda aka harbe shi ya mutu nan take, amma direbansa ya tsira.
Air Vice Marshal Muhammad Maisaka
A ranar 9 ga Nuwamba, 2021, wasu mahara sun kashe Air Vice Marshal Muhammad Maisaka mai ritaya tare da jikansa a gidansa da ke Kaduna.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga gidansa da sanyin safiya suka harbe shi har lahira, sannan suka jikkata direbansa.
Manjo Janar Richard Duru
An yi garkuwa da Richard C. Duru, Manjo Janar mai ritaya, a Owerri, Jihar Imo, a watan Satumba na 2023.
Daga bisani masu garkuwar suka kashe shi duk da cewa an ruwaito cewa an biya dala 50,000 domin fansarsa.
Sai dai daga bisani ƴansanda sun ruwaito cewa sun samu nasarar kama waɗanda suka aikata aika-aikar.
Birgediya Janar Uwem Udokwere
A ranar 23 ga Yuni, 2024, wasu mahara sun kashe Birgediya Janar Uwem Harold Udokwere mai ritaya a gidansa da ke Sunshine Estate, Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa maharan waɗanda ake zargi ɓarayi ne kamar kakakin rundunar ƴansandan Abuja Josephine Adeh ta sanar, sun shiga gidan suka soka masa wuƙa har lahira yayin da yake ƙoƙarin kare iyalinsa.
Kashe Udokwere ya matuƙar ɗaukar hankali, musamman ganin ya auku ne a babban birnin ƙasar, wato Abuja.
Birgediya Janar Maharazu Tsiga
A watan Fabrairu, 2025, an yi garkuwa da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya, wanda tsohon shugaban hukumar yi wa ƙasa hidima ta Najeriya wato NYSC ne.
An sace shi tare da wasu mutane tara a garinsu da ke ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina a yankin arewa maso yammacin ƙasar.
Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, masu garkuwar sun ci gaba da riƙe shi na wasu makonni kafin daga bisani a sake shi a watan Afrilu, 2025.
Kanar Joseph Ajanaku
A watan Janairu, 2026, an yi garkuwa da Kanar Joseph Ajanaku mai ritaya a Jihar Plateau.
An sace shi daga gidansa da ke kusa da cocin Salvation Army a hanyar Rukuba da misalin ƙarfe 12:45 na dare.
Masu garkuwar sun nemi naira miliyan 200 a matsayin kuɗin fansa tare da barazanar kashe shi.
Sai dai daga baya sojoji suka ce sun samu nasarar ceto bayan wani aikin da suka ce sun gudanar na sirri.
Birgediya Janar Musa Uba
A ranar Alhamis 14 ga watan Nuwamban 2015 ce ƙungiyar ISWAP ta kai wani harin kwanton-ɓauna kan ayarin sojojin Najeriya a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno.
Sai dai tun bayan harin, wani abu da ya shige duhu shi ne makomar kwamandan birged na 25, wato Birgediya Janar M. Uba, wanda shi ne jagoran sojojin.
A ranar Asabar 15 ga wata, sai ga shi a ranar Litinin 17 ga wata ƙungiyar ISWAP ta sanar da cewa ta kama tare da hallaka shi.
Duk da cewa ana kokwanto kan mutuwarsam shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar sojan a wata sanarwar jaje da mai magana da yawunsa ya fitar.
Rabe Abubakar
Na kwana-kwanan nan shi ne Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda kuma tsohon mai magana da yawun rundunar tsaro ne.
An yi garkuwa da shi tare da matarsa yayin da suke tafiya zuwa Katsina a ranar 30 ga Mayu, 2026.
Sannan an sanar da cewa ya rasu a hannau ƴanbidiga da suka yi garkuwa da shi a ranar 13 ga Yuni.
Me hakan ke nufi?
Dokta Bulama Bukarti, mai sharhi kan harkokin tsaro a nahiyar Afirka ya shaida wa BBC a wata tattaunawar da ta yi da shi cewa sace manyan sojojin da ƴan bindiga suke yi wata ƴar manuniya ce ga girman matsalar da Najeriya ke fuskanta.
"Wannan wata sabuwar alama ce da ke nuna cewa rashin tsaron Najeriya fa bai bar kowa ba kuma alamu na nuna nan gaba Allah kaɗai ya san mutanen da za ta shafa waɗanda ake ganin shafaffu da mai ne a baya," in ji Bulama.
"idan ba mu manta ba shi fa wannan wanda aka kama shi ne tsohon kakakin sojoji wanda kuka sha yin hira da shi a kan matakan tsaro da ake ɗauka, to idan mutum irin wannan za a sace to me ya ragewa sauran talakawa."
Bulama ya kuma ƙara da cewa abu na biyu da wannan al'amari yake nufi shi ne irin bayanan sirrin da ƴan bindiga ke da shi dangane da al'umma.
"Idan ba suna da masu ba su bayanan sirri ba yaya za a yi ace sun san janar na soji na kan hanya har ma su tare shi?"