AFCON 2019: Shin Najeriya za ta fitar da Afirka ta Kudu?

Nig vs SA

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Daga Mohammed Abdu
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • An wallafa

Senegal ta cire Benin bayan ta doke ta ci 1-0.

Yanzu Senegal ta kai wasan kusa da na karshe ke nan.

Nig vs SA

Asalin hoton, Getty Images

Wannan ne karo na 18 da Najeriya ke halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka, ta kuma lashe shi karo uku, bayan da ta dauka a 1980 da 1994 da kuma 2013.

Haka kuma Super Eagles ta yi ta biyu sau hudu a 1984 da 1988 da 1990 da kuma 2000, kuma sau bakwai ta yi ta uku a 1976 da 1978 da 1992 da 2002 da 2004 da 2006 da kuma 2010.

Nig vs SA

Asalin hoton, Getty Images

Ita kuwa Afirka ta Kudu wannan ne karo na 10 tana halartar gasar cin kofin Afirka inda ta yi nasarar lashe shi sau daya a 1996 a gasar farko da ta fara halarta.

Haka kuma Bafana-Bafana ta kuma taba yin ta biyu a 1998 da kuma mataki na uku a 2000.

Wannan ne karon farko da Najeriya ta dawo buga gasar Afirka, bayan da ba ta halarci wanda aka yi a Equotorial Guinea a 2015 da wanda aka yi a Gabon a 2017 ba.

Sai dai kuma duk da rashin halartar wasa biyu da Najeriya ba ta yi ba, ta kan kai zagayen gab da karshe ko sama da haka a guda 14 daga 17 da ta yi gumurzu.

Nig vs SA

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan Najeriya Odion Ighalo shi ne kan gaba da ya kawo Super Eagles Masar a bana da kwallaye bakwai, ciki har da hudun da ya zura a raga a wasa shida da uku rigis da ya ci Libya a Oktoba.

Ita kuwa kasar Afirka ta Kudu ita ce ta karshe da ta samu tikitin kai wa Masar, bayan da ta je ta doke Libya 2-1 a karawar da suka yi a Tunisia.

Kuma wannan ne karon farko da ta dawo buga wasannin bayan da ta kasa halartar gumurzun da aka yi a Gabon a 2017 wanda Kamaru ce ta zama zakara.

Bafana-Bafana ta kasa yin bajinta a karawar rukuni a gasa hudu daga biyar din da ta halartar baya, sai yanzu a Masar da ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe.

Najeriya ta kawo matakin kifa daya kwale a bana, bayan da ta yi ta biyu a rukuni na biyu biye da Madagascar, wadda ta hada maki bakwai, ita kuwa Super Eagles ta kare da shida.

Kuma Najeriya ta hada maki shidan ne bayan da ta ci Burundi da kuma Guinea kowacce kwallo daya mai ban haushi.

Nig

Asalin hoton, AFcon

Hakan ne ya kai ga fafatawa tsakanin Najeriya da Kamaru a wasan zagaye na biyu, inda ta yi nasara da ci 3-2 a karawar da ta kayatar, kuma daya daga gumurzun da ya zama zakaran gwajin dafi a Masar.

Ita kuwa Afirka ta Kudu ta uku ta yi a rukuni na hudu da maki uku kacal, bayan da ta yi nasara a kan Namibia da ci daya mai ban haushi, sai Ivory Coast da Morocco da kowacce ta yi nasara a kanta da ci daya mai ban haushi.

Da yake wannan ne karo na 18 Super Eagles tana halartar gasar kofin Afirka, kawo yanzu tana ta uku a Afirka sannan ta 45 a jerin jadawalin Fifa na kungiyoyin da ke kan gaba a tamaula.

Ita kuwa Afirka ta Kudu tana ta 14 a Afirka sannan ita ce ta 72 a duniya a jadawalin na Fifa.

A manyan wasa 12 a baya da kasashen biyu suka fafata, Najeriya ta yi nasara a shida, ita kuwa Afirka ta Kudu ta ci biyu da canjaras hudu.

Sun fafata a baya-bayan nan a wasan neman shiga gasar Masar, inda Afirka ta Kudu ta doke Najeriya da ci 2-0 ranar 8 ga watan Junin 2017.

Sai dai kuma a wasa na biyu da suka kara a Afirka ta Kudu kasashen sun tashi ne kunnen doki 1-1 ranar 17 ga watan Nuwambar 2018.

nig

Asalin hoton, Getty Images

Doke Masar da Afirka ta Kudu ta yi ya nuna namijin kokarinta duk da cewa kwallo daya ta ci kuma jumulla a gasar guda biyu ta zura a raga a wasa hudun da ta yi.

Ita kuwa Super Eagles ta zura kwallo biyar a wasa hudun da ta buga a Masar da ya kai ta karawar daf da na kusa da na karshe, kuma Odion Ighalo yana da uku a raga.

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta je Masar da 'yan wasa 23 kuma dukkansu kwararru ne, in banda mai tsaron raga Ikechukwu Ezenwa da ke Katsina United mai buga Premier a gida.

Ita kuwa Afirka ta Kudu kusan 'yan kwallonta a gida ke taka-leda in ban da guda shida da ke wasa a waje.

  • 1. Bongani Zungu da ke wasa a France a kungiyar Amiens
  • 2. Lebo Mothiba da ke wasa a France a kungiyar Strasbourg
  • 3. Thulani Serero da ke wasa a Netherlands a kungiyar Vitesse
  • 4. Kamohelo Mokotjo da ke wasa a Ingila a kungiyar Brentford
  • 5. Percy Tau da ke wasa a Belgium a kungiyar Union Saint-Gilloise
  • 6. Lars Veldwijk da ke wasa a Netherlands a kungiyar Sparta Rotterdam
Nig vs SA

Asalin hoton, Getty Images

Watakila masu horar wa ne za su taka rawar gani tsakanin kasashen a ranar Laraba, inda kocin Najerija Gernot Rohr ya fara aiki cikin watan Agustan 2016.

Ya kuma fara wasan farko inad ya doke Tanzaniya da ci daya mai ban haushi a garin Uyo, ya kuma yi rashin nasara a karon farko ranar 10 ga watan Yunin bara a gida inda Afirka ta Kudu ta yi nasara da ci 2-0.

A ranar 7 ga watan Oktoba, Super Eagles ta zama ta farko a Afirka da ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya, bayan da ta doke Zambia 1-0.

Nig vs SA

Asalin hoton, Getty Images

A ranar 4 ga watan Mayun 2017 aka nada Stuart William Baxter dan kasar Ingila a matsayin kocin tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu, inda ya maye gurbin Ephraim 'Shakes' Mashaba, wanda aka sallama a Disambar 2016.

Salon kwallon Afirka ta Kudu na guje-guje da tamaula ne babu kakkautawa, yayin da Najeriya ta yi suna wajen rike kwallo da shafata.

Da yake kasar Benin ta kai zagayen gab da na kusa da na karshe duk da ta uku ta yi a rukuni na shida, kuma hakan bai hana ta fitar da Morocco ba a karawar zagaye na biyu, za ta buga da Senegal ranar Laraba.

Ita ma Afirka ta Kudu ta uku ta yi a mataki na hudu da maki uku, amma hakan bai hana ta fitar da Masar mai masaukin baki ba.

Shin ko Najeriya za ta iya cire Afirka ta Kudu a ranar ta Laraba?