Da wuya Super Eagles ta kara buga wani wasa a Masar

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan Najeriya na takaddama da hukumar kwallon kafar kasar tun kafin karawa da za ta yi da Guinea a gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar Laraba.
Kawo yanzu babu wani dan wasan Super Eagles da ya karbi alawus ko kuma ladan wasa na dala dubu 10.
Hukumar kwallon kafa ta NFF, na fatan kamo bakin zare ka da 'yan wasa suki fita fafatawa da Guinea ranar Laraba a Masar.
Kocin Najeriya, Gernot Rohr ya ce ''Dalilin da ya sa Ahmed Musa bai halarci taro da 'yan jarida ba ranar Talata, saboda 'yan wasan suna da wani taro a tsakaninsu mai mahimmanci.
''Ina fatan za a shawo kan matsalar, ta yadda za mu fuskanci kalubalen da ke gabanmu.''
'Yan wasan sun yi latti zuwa atisaye na awa daya ranar Talata, kuma suna shirin daukar wasu matakin.
NFF, wadda take karbar kudin bukatunta daga gwamnati ta musanta zargin da ake mata cewar ita ce ta kawo tsaikon biyan alawus-alawus da ladan buga kwallo.
BBC ta fahimci cewa tawagar kwallon kafa ta Najeriya wadda suke tare tun watan Yuni, an yi mata alkawarin baki cewar za a biya su hakkinsu kafan fara gasar kofin nahiyar Afirka.

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ba shi ne karo na farko da 'yan wasan Super Eagles ke kin zuwa atisaye ba, sakamakon kin biyan hakkinsu a lokacin wasu manyan wasannin tamaula.
A gasar cin kofin duniya da aka yi a 2014, 'yan wasan Najeriya sun ki zuwa atisaye kan rashin biyansu hakkinsi, a wasan zagaye na biyu da za ta fafata da Faransa.
Tawagar kwallon kafa ta Mata ta Nijeriya, Super Falcons ta yi bore karo biyu inda ta fara a Afirka ta Kudu da zuwa Abuja kan biyan hakki.
Haka kuma Super Falcons ta nemi hakkinta bayan da aka fitar da kasar a gasar cin kofin duniya a Faransa.











