Messi ya sha kashi a Copa America

Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Colombia ta ba Argentina kashi ci 2-0 a wasan farko na rukuni da suka fafata a gasar lashe Copa America.

Wannan ne karon farko da Colombia ta doke Argentina a shekaru 12.

Roger Martinez da Duvan Zapata ne suka ci wa Colombia kwallayenta a ragar Argentina - tawagar da ke kunshe da Messi da Aguero.

Messi ya ce ba su so farawa da rashin nasara a gasar, amma wannan ba zai nuna cewa sun kariya ba.

Argentina ta lashe kofin sau 14, amma rabon da ta lashe kofin tun 1993.

A zamanin Messi ta kai zagayen karshe sau biyu amma ta gaza lashe kofin.

A wasa na gaba Argentina za ta kara ne da Paraguay.

A ranar Asabar Venezuela da Peru sun rike juna ne 0-0 a rukuninsu na A

Brazil ce ke jagorantar rukunin A bayan ta lallasa Bolivia 3-0.