Tsamar Messi da Ronaldo ba ta kare ba

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ake ban kwana da shekarar 2018, har yanzu Lionel Messi da Cristiano Ronaldo suna kan dabi'ar nan ta rige-rigen zama na daya a yawan cin kwallaye.
An fara adawa tsakanin Messi da Ronaldo a shekarar 2009, lokacin da dan wasan tawagar Portugal ya koma Real Madrid da taka-leda.
Ko da yake Ronaldo ya koma Juventus a farkon kakar bana, 'yan wasan sun ci gaba da cin kwallaye kamar yadda suka saba a kowacce kakar tamaula.
Kawo yanzu Messi ya ci kwallo 14 a gasar La Ligar bana, shi kuwa Ronaldo guda 11 ya ci a Juventus a gasar Serie A.
Messi ya ci wa Argentina kwallo 50, kuma karo na takwas yake haka a shekara, shi kuwa Ronaldo kwallo 46 ya ci wa Portugal a 2018.
Messi ya zura kwallo 567 a raga, Ronaldo kuwa yana da 542.
A shekarar nan da za ta kare Lewandowski yana da kwallo 54 a raga, sai Salah da 41 da Harry Kane mai 38 da kuma Luis Suarez mai 37.






