PSG ta dauki kofin Ligue 1 bayan doke Monaco 7-1

'Yan wasan PSG na murna

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wannan ne karo na biyar da Paris St-Germain ta ci kofin gasar Ligue 1 a kaka shida
An wallafa

Paris St-Germain ta dauki kofin gasar Faransa, Ligue 1 bayan da ta lallasa masu rike da kofin Monaco 7-1 a filin Parc des Princes.

Yadda 'yan wasan kungiyar mallakar Qatar suka nuna iyawa da bajinta ya sa suka yi wannan nasara ta yankan shakku wadda ta sa suka ba wa Monacon ta biyu a tebur tazarar maki 17, kafin kammala gasar da wasa biyar.

Giovani lo Celso da Angel di Maria kowanne ya ci bibbiyu, yayin da Edinson Cavani da Julian Draxler kowa ya saka daidai a raga.

Angel di Maria lokacin da yake cin Monaco

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Angel di Maria ya ci wa PSG bal 14 gaba daya a kakar nan, biyu daga ciki ya zura a ragar Monaco

Radamel Falcao na Monaco shi ya ci kansu ta bakwai din, yayin da Rony Lopes ya ci musu ladan-gabe, guda daya a wasan da za a ce bangare daya ne ya yi rawar-gani.

Kofin shi ne na biyar na gasar ta Faransa, Ligue 1 da PSG ta ci a cikin kaka shida.

PSG ta dawo da karfinta ke nan.

Monaco ta dauki kofinta na farko ne a cikin shekara 17 a kakar 2016-17, bisa jagoranci ko kokarin Falcao da kuma zuwan matashin dan wasan Faransa Kylian Mbappe.

Falcao ya ci gaba da zama a Monaco, amma Mbappe - wanda ya koma PSG a kan fam miliyan 166, farko a yarjejeniyar aro, da kuma wasu manyan 'yan wasan kamar dan baya Benjamin Mendy sun bar kungiyar a bazarar da ta wuce.

Wannan tafiya ta tarin gwanayen 'yan wasan ta raunana Monaco wadda ita ce mafi karfi cikin abokan hamayyar PSG.

Wannan ne ya sa kusan a ce ba makawa kungiyar ta Paris za ta sake zama zakara a Faransa.

PSG ta doke Monaco 3-0 a wasan karshe na cin kofin kalubale na lig na Faransa ( French League Cup), a karshen watan da ya gabata, sai kuma ga shi a wannan karon lallasawar ta ma fi waccan.

Mece ce makomar kociya Unai Emery da Neymar yanzu a PSG?

PSG ta dauki tsohon kociyan na Sevilla Unai Emery a matsayin sabon mai horas da 'yan wasanta tsawon shekara biyu a watan Yuni na 2016, kuma cikin kaka daya yanzu ya dauki kofi.

To amma takaicin fitar da su da Real Madrid ta yi daga gasar Zakarun Turai ta sa ake tababar ci gaba da zaman kociyan a kungiyar.

Har ma ana ganin Emery zai bar kungiyar a karshen kakar nan, kuma tsohon kociyan Borussia Dortmund Thomas Tuchel shi ake rade-radin zai maye gurbinsa.

Neymar fa?

Shi ma Neymar ana ta maganganu kan yuwuwar ci gaba da zamansa a PSG din a 'yan watannin da suka gabata.

Neymar ya koma PSG ne daga Barcelona a kan kudin da ba a taba sayen wani dan wasa ba a duniya har fam miliyan 200 a watan Agusta, kuma daga zuwansa ya ci musu kwallo 28 a wasa 30 da ya yi.

Dan wasan mai shekara 26 ba ya cikin tawagar kungiyar da ta doke Monaco ta dauki kofin saboda raunin da yake can yake jinya, wanda ya ji a watan Fabrairu, a idon sawunsa.

Duk da irin bajintar da ya nuna a kakarsa ta farko ana rade-radin cewa dan wasan ba ya jin dadin zamansa a kungiyar ta Paris.

Yanzu kusan a duk mako ana danganta shi da tafiya kungiyar La Liga Real Madrid.